Daga Imrana Abdullahi, Kaduna arewacin Najeriya
Hukumar kula da ilimin fasaha ta tarayyar Najeriya (NBTE), ta roki Gwamnatin tarayya da ta ware karin kudade ga ilimin fasaha a kasar nan.
Daraktan shirye-shirye na hukumar ta NBTE, Arch Ngbede Ogoh ne ya yi wannan roko a lokacin da ya jagoranci tawagar da ta duba albarkatun shirye-shirye guda goma a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke garin Daura a Jihar Katsina.
Ya ce samun sana’o’i ya zama babban abin da ake bukata ga duk wani ci gaban tattalin arziki mai dorewa na al’umma, kuma a lokuta da dama ana kallon ilimin kwalejin kimiyyar da fasaha a matsayin wuri mafi dacewa ga matasa wajen bunkasa fasaharsu da iliminsu.
Wannan a cewarsa, ya bayyana bukatar samun karin kudade ga kwalejojin Koyar da ilimin kimiyya da fasaha tare da tsadar kayan aiki, ta yadda matasa da dama za su samu damar koyon sana’o’in dogaro da kai da kuma bunkasa kansu.
“Don haka ne muke kira ga gwamnati da ta kara yawan kudade ga duk kwalejin kimiyya da fasaha a fadin kasar nan don kasancewa cikin mafi kyawu a duniya”, in ji shi.
Tun da farko, shugaban kwalejin, Farfesa Aliyu Mamman, ya ce matashiyar kwalejin ta nemi amincewar shirye-shiryen guda Goma bisa la’akari da hargitsi da roko da wani dan al’umma da ke neman a yi amfani da su yadda ya kamata domin samar da ababen more rayuwa.