— Ya ce a 1976 GDP ya ninka na China sau uku, ya kuma ninka na Malaysia sau biyu a 1966
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr. Gbenga Hashim, ya soki yadda Najeriya ke ci gaba da dogaro da shawarwarin tattalin arziki na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), yana mai cewa durkushewar tattalin arzikin kasar ta samo asali ne daga manufofin da cibiyoyin waje suka tsara maimakon wadanda suka dace da yanayin cikin gida.
Hashim ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin ARISE TV na karfe 8 na dare, inda ya tattauna kan tattalin arzikin Najeriya, ci gaban kasa, da kuma shirin sa na gina tattalin arziki da darajarsa za ta kai dala tiriliyan 4.
A cewarsa, Najeriya ta fi yin nasara lokacin da take aiwatar da manufofin tattalin arziki masu cin gashin kai, yana mai kawo misalin matsayin tattalin arzikin kasar a shekarun 1970.
“Lokacin da Najeriya ba ta bin IMF gaba daya ba, GDP a 1976 ya ninka na China sau uku, haka kuma GDP dinmu ya ninka na Malaysia sau biyu a 1966,” in ji shi.
GDP dai wani alama ne da masana tattalin arzikin k’asashe ke la’akari da shi wajen auna arzikin k’asa.
Hashim ya kara da cewa, “Babu wata kasa mai muhimmanci da ke hadiye duk magungunan da IMF ke bayarwa.” Ya jaddada cewa IMF ba mai zuba jari ba ce, don haka hasashenta bai kamata ya zama babban ma’aunin ci gaban kasa ba.
Hashim ya ce ainihin ma’aunin nasarar tattalin arziki shi ne yadda rayuwar al’umma take inganta, ba wai alkaluman ci gaba kadai ba.
Dan takarar na PDP ya kuma yi watsi da murnar da Gwamnatin Tarayya ke yi kan ci gaban GDP na kashi hudu, yana mai cewa hakan bai isa ba idan aka yi la’akari da asarar tattalin arziki da aka samu a ‘yan shekarun nan.
“Bayan an rage GDP da kusan kashi 50, ci gaban kashi hudu har yanzu yana nuna koma baya. GDP ya ragu daga dala biliyan 574 a 2014 zuwa dala biliyan 230 a yanzu,” in ji shi, yana mai cewa gwamnatin All Progressives Congress (APC) ba za ta iya ikirarin samun ci gaba ba har sai tattalin arzikin Najeriya ya zarce matakin da ta gada a 2015.
Ya kwatanta hakan da zamanin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, inda ya ce Najeriya ta samu daidaitaccen ci gaban tattalin arziki tsakanin 1999 da 2003.
“Lokacin da Obasanjo ya hau mulki a 1999, Najeriya ta samu ci gaban kashi 5.5 a 2000, amma zuwa 2003 kasar na samun kashi 9.5,” in ji shi, yana mai dagewa cewa duk da kura-kuranta, PDP ta fi APC aiki a fannoni da dama.
Hashim ya kuma soki abin da ya kira gazawar APC a bangaren wutar lantarki, yana zargin cewa gwamnatin ba ta kara ko megawatt guda ba cikin shekaru 10 da suka gabata.
“APC ba ta kara ko megawatt daya na wutar lantarki ba cikin shekaru 10,” in ji shi. Ya kuma yi zargin cewa maimakon fadada tattalin arziki, gwamnatin ta jagoranci koma baya.
“APC ba ta kara dala daya a GDP na Najeriya ba; maimakon haka ta lalata kusan kashi 50 na tattalin arzikinmu cikin shekaru 10,” ya kara da cewa.
A bangaren noma kuwa, Hashim ya ce Najeriya ta yi asarar kusan dala biliyan 4 na jarin samarwa cikin shekaru biyu a karkashin Shugaba Bola Tinubu, yana danganta hakan da yunkurin da ya kira na “tilasta saukar farashin abinci,” wanda ya ce ya raunana manoma tare da dagula tsarin samar da kayayyaki.
Ya ce tattalin arzikin kasar na bukatar ci gaba mai lamba biyu (double-digit growth) domin ya farfado, ba karamin ci gaba da ya kira na “maras tasiri” daga gyare-gyaren da suka gaza ba.
“Babban rage darajar Naira ya fara tun 1986; babu wani sabon abu ko kirkira a ciki,” in ji shi. Hashim ya kara da cewa tattalin arzikin Najeriya na bukatar wani shiri irin na John Maynard Keynes ko kuma irin tsare-tsaren jarumtaka na Roosevelt domin farfado da tattalin arzikin da ya shiga mawuyacin hali.
Da yake tsokaci kan kisan gillar da aka yi a al’ummar Woro da ke karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, inda aka rawaito cewa kusan mutane 200 suka mutu, Hashim ya bayyana lamarin a matsayin babbar gazawar tsaro ta kasa.
Ya tambayi dalilin da ya sa jami’an tsaro suka kasa kai dauki duk da kusancin sansanin Sojojin Sama.
“Duk da cewa akwai sansanin Sojojin Sama da ke tazarar mintuna 15 kacal, an bar ‘yan ta’adda suka shiga suka kashe kusan mutane 200 ba tare da wata turjiya daga gwamnati ba,” in ji shi.
Hashim ya ce lamarin ya wuce gazawar tsaro kawai, yana mai cewa hakan na tayar da tambayoyi masu tayar da hankali kan yiwuwar akwai masu hannu a ciki.
THESHIELD Garkuwa