Home / Labarai / MUNA SON ABA JAMI’AN TSARO CIKAKKEN HADIN KAI – YAHAYA MAHUTA

MUNA SON ABA JAMI’AN TSARO CIKAKKEN HADIN KAI – YAHAYA MAHUTA

Daga Imrana Abdullahi
Yahaya Nuhu Mahuta, dan majalisa ne a majalisar dokokin Jihar Katsina ya bayyana kudirinsa na ganin ya taimakawa Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Dokta Dikko Umar Radda wajen bunkasa harkokin ilimi a Jihar.
Yahaya Nuhu Mahuta ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Yahaya Nuhu ya ci gaba da bayanin cewa samar da ingantaccen ilimi musamman ga mutanen karkara zai taimaka matuka wajen yin maganin matsalar tsaron da ake fuskanta a halin yanzu.
“Saboda an tabbatar da cewa a halin da ake ciki a yanzu wadanda suka koma cikin dazukan kasar nan suna aikata ayyukan aika aika da suka hada da satar mutane domin karbar kudin fansa da sauran ayyukan ta’addanci duk suna faruwa ne sakamakon matsalar rashin ilimin da irin wadannan mutanen ke fuskanta tun suna kananan har tasowarsu”.
Yahaya ya kara da cewa amma da irin matakan da Gwamnatin  Dokta Dikko Umar Radda take dauka domin ganin sun magance matsalar tsaron da ake fuskanta hakika lamarin zai zama sai tarihi da ikon Allah.
“Mun yi gagarumin taro a kan matsalar tsaro a matakin Jiha kuma mun dawo a matakin kananan hukumomi mun yi taro gagarumi irinsa kuma mun yi wani taron da shugaban karamar hukuma da kuma jama’ar da suka kamata domin zabo mutanen da za a yi aiki tare da su a wajen maganin matsalar tsaron da ake fuskanta.
“Kuma abin farin ciki a halin yanzu shi ne yadda jama’ar karamar hukumar Dandume ke Bacci da idanunsu a rufe kuma a cikin gidajensu ba kamar can baya ba da wasu da yawa ke kwana a cikin Dazuka sai gari ya waye su dawo cikin gidajensu wannan abin farin ciki ne da harkar tsaron ta fara inganta a karamar hukumar Dandume da Jihar Katsian baki daya”, inji Yahaya Mahuta.
Kuma a matsayina na dan majalisa ina yin kira ga daukacin al’ummar karamar hukumar Dandume da Jihar Katsina baki daya da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro domin samun kwalliya ta biya kudin sabulu.
“Saboda kamar yadda kowa ya Sani sai da ingantaccen tsaro ne kowace irin harka ta rayuwa za ta iya gudana”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.