Home / Labarai / Gwamnan Bauchi Ya Sauke Shugabannin Rikon Karamar Hukumar

Gwamnan Bauchi Ya Sauke Shugabannin Rikon Karamar Hukumar

Daga Imrana Abdullahi
 Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya rusa dukkan kwamitocin riko na kananan hukumomi ba tare da bata lokaci ba sakamakon karewar wa’adinsu na ofis.
 Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Muhammad Kashim ne ya mika takardar amincewar gwamna Bala Muhammad a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Bauchi.
 A cewar sanarwar, don haka an umurci kwamitocin riko na shugabannin kananan hukumomin da su mika al’amuran kananan hukumomin ga shugabannin hukumominsu har sai an nada kwamitocin riko.
 Bala Mohammed ya kuma yi wa daukacin ‘yan kwamitin riko na kananan hukumomi fatan samun nasara a ayyukansu na gaba tare da gode musu da wannan gudunmawar da suka bayar.

About andiya

Check Also

NA 8 Div Sokoto new GOC,  General Ibikunle assumes

S. Adamu, Sokoto A new GOC for the 8 Division Nigerian Army, Sokoto , appointed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.