Home / News / Jam’iyyar PDP ta zabi Hon Yusuf Dingyadi a matsayin wakili na kwamitin musamman a kan yan jarida da watsa labarai na zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da Imo

Jam’iyyar PDP ta zabi Hon Yusuf Dingyadi a matsayin wakili na kwamitin musamman a kan yan jarida da watsa labarai na zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da Imo

Daga Imrana Abdullahi
Jam’iyyar PDP ta Kasa ta baiyana nadin Honarabul Yusuf Abubakar Dingyadi a matsayin wakili a cikin kwamitin musamman da zai lura da harakokin hulda da yan jaridu da Watsa labarai na zaben gwamnonin jihohin Bayelsa, Kogi da Imo wanda ake sa ran gudanarwa a tsakanin watanin Nuwamba da Disamba na wannan shekara.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Honarabul  Debo Olugangba
Babban Sakataren Watsa labarai na jam’iyyar PDP na Kasa da shi kansa Yusuf Dingyadi ya aikewa da wakilin mu.
Haka kuma PDP ta baiyana sunayen sauran wakilan guda Goma sha Tara wadanda suka kunshi, Sakataren Watsa labarai na PDP na kasa;  Mr Debo Ologunagba a matsayin shugaba da Mr Richard Ihediwa wanda zai kasance sakatare, yayin da sauran membobin sun kunshi Mr Kola Ologbondiyan da Hon Emmanuel Ibeshi da Ibrahim Abdullahi da Otunba Segun Sawunmi da Osaro Onaiwu da Abdul M Bashir da sauransu.
Malam Yusuf Dingyadi wanda shine babban mataimaki na mussaman ga Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa (SSA) akan watsa labarai da sadarwa ya taba rike mukamin mataimakin daraktan labarai da yan jarida na kamfen din Atiku/Okowa a yankin Arewa a zaben da ya gabata.
Ana sa ran kaddamar da wannan kwamitin na mussaman a Abuja nan gaba kadan.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.