Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta yi barazanar fara yajin aikin sai baba-ya-gani, idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun ta a karshen wa’adin kwanaki 21 da ta gindaya.
Tun farko dai kungiyar ta bayar da wa’adin ne a ranar 1 ga watan Satumba kan wani jinkiri da gwamnati ta yi na aiwatar da matakan da suka dace domin dakile illolin cire tallafin man fetur.
Daga bisani kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu tsakanin ranar 5 zuwa 6 ga watan Satumba domin nuna muhimmancinta.
Sai dai da yake magana yayin wata tattaunawa da jaridar Punch a ranar Talata, mataimakin babban sakataren kungiyar ta NLC, Christopher Onyeka, ya ce yajin aikin ya biyo bayan halin ko in kula da gwamnati ke yi na biyan bukatun ma’aikatan Najeriya.
Ya yi bayanin cewa matakin masana’antu, wanda zai iya farawa kowace rana a mako mai zuwa, zai haifar da dakatar da ayyukan kasuwanci da tattalin arziki a fadin kasar nan har sai abin da hali ya yi.
Sakataren kungiyar ta NLC ya kara zargin gwamnatin tarayya da ficewa daga teburin tattaunawar.
Ya ce: “Mun aika da wasikar zuwa ga Gwamnatin Tarayya a ranar 1 ga Satumba, 2023, don haka zuwa ranar 22 ga Satumba, 2023, wa’adin kwanaki 21 zai kare.
“Mun bayyana karara cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da batun kuma ta fice daga teburin tattaunawar da ake yi; Gwamnatin ta daina tattaunawa da ’yan Najeriya kuma babu wata tattaunawa ta gaskiya da ke gudana.
“Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin shi kadai a gidan talabijin da Shugaban NLC, Joe Ajaero, cewa zai sake fasalin kwamitocin, amma bai yi haka ba, kuma tun a wancan lokaci kwamitocin ba su hadu ba kuma babu tattaunawar da ke gudana. Kamar yadda yake, NLC ba ta tattaunawa da gwamnati,” in ji Mista Onyeka.