.... Ya maye gurbin mataimakin gwamna 4 na bankin koli
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dokta Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a yammacin ranar Juma’ar nan, Cardoso zai yi wa’adi na tsawon shekaru biyar (5) ne a matakin farko, har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da shi.
“Wannan umarni ya yi daidai da sashe na 8 (1) na dokar babban bankin Najeriya na shekarar 2007, wanda ya baiwa shugaban tarayyar Najeriya ikon nada gwamna da mataimakan gwamnan hudu (4) a tsakiya.
“Bugu da kari kuma, shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mataimakan gwamnoni hudu na babban bankin Najeriya (CBN), na tsawon shekaru biyar (5) a matakin farko, har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da su,” inji shi.
Sabbin mataimakan gwamnonin sun hada da Misis Emem Nnana Usoro, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Mista Philip Ikeazor, da Dr. Bala M. Bello.
“A bisa tsarin sabunta bege na Shugaba Bola Tinubu, shugaban ya na fatan wadanda aka zaba a sama za su samu nasarar aiwatar da muhimman gyare-gyare a babban bankin Najeriya, wanda zai kara kwarin gwiwar ‘yan Najeriya da abokan huldar kasa da kasa wajen sake fasalin tattalin arzikin Najeriya wajen samun ci gaba mai dorewa. da wadata ga kowa da kowa,” in ji Ngelale.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ruwaito cewa tun bayan dakatar da Mista Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya CBN a watan Yuni, mataimakin gwamnan bankin, Faloshodun Shonubi, ya kasance mukaddashin gwamnan babban bankin.