Home / Labarai / Maulud: Sanata Adamu Ya Taya Musulmi Murnar Bikin Maulidin Annabi Muhammadu (S.A.W)

Maulud: Sanata Adamu Ya Taya Musulmi Murnar Bikin Maulidin Annabi Muhammadu (S.A.W)

Daga Imrana Abdullahi
Sanatan da ke wakiltar al’ummar yankin Kaduna ta tsakiya a Jihar Kaduna ya bukaci daukacin musulmai da du yi koyi da halayen fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).
Sanata Lawal Adamu Usman da ake yi wa lakabi da Mista LA, ya yi wannan kiran ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sakon tara murnar Maulidin.
Sanata Lawal Adamu, wanda shi ne shugaban kwamitin ilimi na majalisar Dattawan Najeriya ya ce a lokacin da al’ummar musulmi ke bikin murnar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi don haka ne a madadinsa da jama’ar da yake wakilta a majalisa ya na taya daukacin Musulmin Jihar Kaduna, Najeriya da duniya baki daya murnar wannan muhimmiyar rana da ake bikin Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).
Sanata Adamu ya ci gaba da cewa wannan muhimmin lokaci ne ba ne don haka muke yin kira ga daukacin al’umma da su kara kaimin yin addu’o’in samun zaman lafiya, magance matsalar tsaron da ke zama kalubale, matsalar kakanikayi da aka shiga ciki da kuma Rabe raben kawunan jama’a da ake fama da shi a wadansu yankuna na kasa.
Ya ce; a lokacin da muke bikin murnar fiyayyen halitta mai gaskiya da rikon Amana Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, hakika akwai bukatar da ke akwai na ganin mun yi duba da abin da ke faruwa na kalubale iri iri musamman na tabarbarewar halin rayuwa da ke addabar al’umma marasa karfi, wanda kafar yadda kowa ya Sani rayuwarsa ta kasance ba komai ba, mutane na cikin wani mawuyacin hali duk da irin dimbin tattalin arzikin da muke da shi a kasa.
Saboda haka, “nake bayar da shawara a gare mu duk baki daya da mu ajiye batun siyasa a gefe guda mu dubi sauran wadansu mutanen da suke cikin matsalar tabarbarewar halin rayuwa, da nufin a taimaka, a kuma yi addu’ar neman dauki na samun sauki daga madaukakin Sarki Allah domin samun ingantar harkokin rayuwarsu kuma a hakan sai a ci gaba da yin addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da taimakon Juna a kasa baki daya”, inji Mista LA.
Sai ya kuma kara yin kira ga daukacin al’ummar musulmi da su ci gaba da yin koyi da hali da kuma karantarwar Annabi Muhammadu sallalahu alaihi wasallam, da nufin yin yafiya, aminci da taimakon Juna musamman ga marasa karfin da suke a cikin al’umma domin kasar ta Inganta.
Sai ya bayar da tabbaci ga jama’ar mazabarsa da cewa za su samu cin moriyar gagaruman ayyukan raya kasa da inganta rayuwarsu musamman ma ga karasa karfi saboda haka sai ya yi kira ga jama’a da su zauna lafiya domin samun sauki a cikin al’amuran rayuwarsu.
Ssi ya yi alkawarin samar da taimako mai dimbin yawa musamman ga bangarorin tsaro, Ilimi, lafiya da samar da ababen more rayuwa domin walwalar jama’a da kuma samar da ingantattun tituna duk a cikin dan kankanin lokaci.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.