….An Yi Kira Ga Daukacin Yayan Jam’iyyar PDP Na Jihar Katsina Da Su Tabbatar Da Hadin Kai A Tsakaninsu
Daga Imrana Abdullahi
Shugaban jam’iyyar PDP reshen Arewa maso Yamma Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya bayyana samun hadin kai a tsakanin yayan jam’iyyar PDP a shiyyar musamman a tsakanin yayan jam’iyyar na Jihar Katsina da su hada kansu domin samun kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sanata Bello Hayatu Gwarzo, ya yi wannan kiran ne a wajen taron tattaunawa da ake yi tsakanin shugabannin PDP na shiyyar Arewa da kuma shugabannin PDP na Jihar Katsina kamar yadda jam’iyyar ta bayar da umarnin a zauna da shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma a ofishin jam’iyyar da ke Kaduna.
“Samun cikakken hadin kai da taimakon Juna musamman ga Dattawan jam’iyya da kuma masu hannu da shuni su taimakawa masu rike da shugabancin jam’iyyar a Jiha da nufin samun ciyar da jam’iyyar gaba”.
Jam’iyyar PDP dai na da babbar dama a Jihar Katsina kuma jiha ce da kowa ya Sani ba ta da rikicin siyasa a duk lokacin zabe da kuma kowane lokaci idan aka yi maganar siyasa a tsarin dimokuradiyya”.
” idan aka samu hadin kai da taimakekeniya komai zai ta fi dai- dai kamar yadda ake bukatar a samu”