Daga Imrana Abdullahi
Hajiya A’ishatu Ibrahim Madina, yar takarar neman kujerar shugabar mata ta kasa a jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta tabbatar da kare martaba da mutuncin mata idan Allah ya bata wannan matsayin karkashin PDP.
A’ishatu Madina ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu a garin Kaduna.
Madina ta ce cancantar da take da ita ne ya Sanya aka ce ta fito neman wannan kujera ta shugabancin mata a mataki ma kasa, kasancewar ta yi shugabancin mata a PDP reshen Jihar Kaduna kuma ta yi shugabancin mata a matakin shiyya don haka ne ake ganin za ta iya ci gaba da bayar da gudunmawa a mataki na kasa.
” wannan neman shugabancin matan PDP ba wai domin gaban kaina na yi ba saboda akwai dimbin masoya da yawa har ma wadanda suke ganin mun yi shugabanci a can baya kuma lamarin ya yi masu dadi don haka suka nemi mu tsaya wannan takarar idan Allah ya sa za a kawo shi Arewa maso Yamma ya zama in fito nema.
Ta ci gaba da cewa dalili shi ne da can an yi shugabanci a baya a da sanin tafiyar da al’amuran mata da kuma shugabancin da muka yi musamman siyasar jam’iyya ta yadda za a motsa jam’iyyar ayi Gwagwarmaya musamman a fannin shugabancin mata a matakin kasa baki daya ta yadda za a iya kawo ingantaccen wakilcin mata a tsarin siyasar jam’iyya da kasa baki daya.
” Akwai abubuwa da dama da ake yi da suka shafi mata amma idan babu kyakkyawan wakilcin mata sai kaga an samu rauni wajen aiwatarwa da samun wakilcin mata, a cikin al’amuran mata da suke faruwa na yau da kullum a ciki da wajen jam’iyya.
Sabida haka zan tabbatar an samu ingantaccen shugabanci a bangaren mata da tafiyar da harkokinsu jam’iyyar PDP a matakin kasa da duk inda ya dace.