Home / Labarai / Muna Bukatar Kudin Bai Daya A Afirka – Sarkin Buzayen Ghana

Muna Bukatar Kudin Bai Daya A Afirka – Sarkin Buzayen Ghana

 

Daga Imrana Abdullahi
An bayyana bukatar ganin an samu kudin da za a rika kashewa ana yin amfani da su a dukkan fadin nahiyar Afirka baki daya.
Sarkin Buzayen Ghana Abubakar Sadiq ne ya yi wannan kiran na a samu hadin kai a baki dayan nahiyar Afirka baki daya wanda zai ba yankin damar su rika yin amfani da kudin bai daya a kowace kasa da ke nahiyar.
Sarkin Buzaye Abubakar ya dai bayyan hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala karon kaddamar da shugabanni na kasa na kungiyar A A Charity Foundation da kuma bayar da tallafin marayu da kungiyar A A Charity Foundation ta yi a garin Kaduna.
Abubakar ya ci gaba da cewa a halin yanzu babu abin da nahiyar Afirka ke bukata da ya wuce samun ingantaccen sahihin hadin kai a tsakanin al’ummar yankin Maza da mata yara da manya, tsofaffi da matasa wanda hakan zai samar da ci gaban da aka dade ana matakin za a samu a yankin nahiyar Afirka baki daya.
“Ta yaya ni a can ina kasar Ghana wanda daga can na samu halartar wannan taron kungiyar mai kokarin inganta rayuwar jama’a Maza da maza, sai na ga a nan Najeriya ma kudinsu ya lalace a Ghana ma kudin ya lalace babu daraja sosai kuma haka abin yake a kusan dukkan kasashen da ke nahiyar Afirka baki daya, ko ina kudinsu ba shi da daraja, sai kaga Dalar Amurka guda daya amma sai an bayar da makudan kudin Afirka da yawa saboda kudin bashi da daraja sam”.
Duba da irin wannan ne ni nake ganin hakika ya dace ayi kudin Afirka bai daya da za a rika kashewa a yankin baki daya kowace kasa kaje zaka iya kashe wannan kudin na Afirka hakan zai taimaka a daina samun matsalar hauhawar farashin dalar Amurka baki daya.
“Ni a nawa hangen ya dace a rika yin amfani da kudin Najeriya a kowace kasa da ke Afirka, kasancewar Najeriya ce Uba a duk yankin nahiyar Afirkan nan don haka sai taimaka wa yankin”.
Hadin kai dai shi ne babban abin yi da kowa ya dace ya tabbatar ya bada tasa gudunmawar a samu ci gaban yankin

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.