Home / KUNGIYOYI / Kungiyar A A Charity Foundation Ta Karrama Gwamna Uba Sani

Kungiyar A A Charity Foundation Ta Karrama Gwamna Uba Sani

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon lura da irin Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ke aiwatar da ayyukan ci gaban rayuwar al’umma musamman ma Talakawan Jihar yasa Kungiyar A A Charity Foundation ta Karrama Gwamnan.

An dai karrama Gwamnan ne a wajen babban taron kungiyar na kasa inda aka kaddamar da wadanda aka Dorawa alhakin tafiyar da shugabancin kungiyar karkashin babbar jagora Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad.

Gwamnan Wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada ya wakilta kuma ya karbi karramawar a madadinsa ya bayyana farin ciki da gamsuwa game da abin da kungiyar A A Charity Foundation ke yi wa al’umma musamman ma talakawan da ke da bukatar hakan.

Kungiyar A A Charity Foundation dai na taimakawa al’umma ne da suka hada da marayu, marasa galihu, yara da manya masa da mata da suka hada da masu bukata ta musamman domin rayuwarsu ta inganta.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.