Daga Imrana Abdullahi
Labarin da muke samu da dumi duminsa a yanzun nan na cewa tsohon shugaban marasa rinjaye kuma fitaccen mai taimakawa rayuwar al’umma da kishin kasa da addininsa Honarabul Muhammadu Ali, da ya taba zama dan majalisa mai wakiltar Mazabar Kawo a cikin garin Kaduna.
Kamar dai yadda kowa ya Sani ne dan majalisa Muhammadu Ali, ya zama dan majalisa ne a karkashin tutar jam’iyyar CPC, wanda a lokacin ba a samu wata kujerar da ke yiwa dimbin al’umma Maza da Mata Yara da Manya aikin taimako su zama mutanen da suma za su dogara da kansu ba kamar wakilcin da Mihammadu Ali ya yi ba, kuma har yanzu ma ya na kokarin ci gaba da koyawa jama’a sana’o’i.
A wannan lokacin ne yan uwansa yan majalisa daga wasu Jihohi daban daban na arewacin Najeriya kai har ma da Sojoji daga Jihar Legas duk sun zo domin ganin irin abin da ake cewa dan majalisa ne wannan ke yi wa jama’a.
A misali wata tawagar yan majalisa daga Jihar Jigawa a wancan lokacin sun zo wurin da Muhammadu Ali ya samar da cibiyar koyawa jama’a sana’o’i da karatu domin su gani da nufin suma suje mazabunsu su aiwatar bayan sun yi masa tambayoyi ya kuma ba su amsar da ta dace.
Dan majalisa Honarabul Muhammadu Ali da ya zamanto gagarabadau wanda har yanzu an kasa mayar da kamansa, saboda shi a kullum baya gudun jama’a koda yake a matsayin dan majalisa a kullum ya na ofishinsa inda nan ne ainihin cibiyar koyawa jama’a karatu da sana’a da ke ginin gidan Maggi ko gidan Mamman Jalo a unguwar NDA cikin garin Kaduna.
Honarabul Mihammad Ali ya koyawa jama’a da dama karatun na’ura mai kwakwalwa wato Kwamfuta har wasu sun je sun yi karatu a jami’ar karatu daga gida ta Gwamnatin tarayya a reshen ta da ke Kaduna da kuma koyawa dimbin jama’a sana’ar yin Fenti,dinki,Saka,hada Yogut na sha da dai sauransu
Banda wadanda suka amfana da zuwa karatu kasashen waje inda akwai lokacin da ya na dan majalisa ya samu dama a wata jami’ar kasar waje ta ce ya samo yara matasa da suke da shaidar da za ta ba si damar yin karatun Likita har mutum Goma su za su dauki nauyin karatunsu har su Gama karatun.
Kai Honarabul Muhammad Ali ne dan majalisar da yake da wadansu tsare tsare da asibitoci a duk wata yake tura masu marasa lafiya shi kuma karshen wata ya biya kudin duba lafiya da magungunan da aka yi masu a asibitocin duk ya na yin wannan ne fa kyauata Ruwan Allah, da zuciyar taimakawa bayanin Allah masu bukata.
Shi ne dan majalisar da ke yi wa marasa galihu gata ya samar masu da motar zuwa makaranta a rika kai su makaranta ana kuma dauko su a dawo da su gidajensu a kullum kyauta, kuma shi ne dan majalisar da ke taimakawa al’amuran tsaron al’umma domin baya bari wani abu ya cutar da su ko kadan.
Kai Honarabul Muhammadu Ali ne wanda da zuwansu majalisar dokokin Jihar Kaduna ya tashi ya gabatar da jawabi nan take wani dan uwansa dan majalisa da ba ma jam’iyyar su daya ba ya ce hakika ya samu abokin tafiya da zai yi aiki tare da shi.
Honarabul Mihammadu Ali ne ya jagoranci hana kashe kudin Jihar Kaduna haka kawai don a sayawa yan majalisa motar da sai an Sanya kwamfuta za a iya gyara komai kankantarsa a jikin motar duk da an nuna masa akwai wasu shafaffu da mai da suke da bukata a harkar amma kasancewarsa dan majalisa kuma shugaban kwamitin da sai ya amince a sayi motocin ga yan majalisa ya ce sam ba ta sabuwa, kuma a wannan lokacin haka Gwamna a lokaci marigayi Patrick Ibrahim Yakowa ya goya masa baya sai dai aka canza wasu motocin.
Kai dan kankanin lokqci dai ba zai bari a lissafa irin ayyukan da Muhammadu Ali yake aiwatarwa ba domin al’umma ta ci gaba ba.
Ku ka Sani har yanzu wannan cibiyar na nan ana gudanar da ayyukan raya al’umma dai- dai Gwargwado.
Don haka muke ganin in dai Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani zai yi tafiya da masu son ci gaban Jihar Kaduna, lallai tun da Allah ya bashi Muhammadu Ali, magana ta kare, in dai za a yi domin Allah ba wata tantama ko kadan.