Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Abubakar Musa Umar wani Amini kuma abokin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashin Shettima, ya bayyana mataimakin shugaban kasa da cewa mutum ne wanda a koda yaushe ke son ganin walwala da jin dadi tare da ci gaban al’umma.
Abubakar Musa Umar, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna wajen kaddamar da kayan Noma da suka hada da taraktoci, Takin Zamani da kuma kaddamar da bayar da horo ga wadansu zababbun matasa guda hamsin, hamsin daga Jihohi Goma da gidauniyar Kashin Shettima ta dauki nauyi kuma mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kansa a Kaduna.
Saboda haka wannan kokarin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi bai zo Mani da mamaki ba domin daman can ni na san shi da son jama’a da kuma son a kyautata masu a koda yaushe.
” Mutum ne da yake a koda yaushe burinsa shi ne al’ummarsa ta ci gaba a fita daga cikin halin rayuwa na matsi da talauci don haka wannan shirin da ya fito da shi hakika ba abin mamaki ba ne ga wadanda suka san shi a kud da kud, wato kusa da kusa. Mutum ne a koda yaushe duk abin da yake da shi na al’umma ne ba wai na sa shi kadai ba domin ya rigaya ya sadaukar da kansa da kuma dukiyarsa ga harkar al’umma saboda haka muna yi wa Allah godiya kuma muna yi masa godiya domin abin da ya yi zai sa mutane su tsaya da kansu a kan kafafunsa har ya dauki ma’aikata a samu ci gaba koda Gwamnati za ta yi maganar bayar da aiki za a tarar ya na da sana’arsa da ta yi masa komai ya na rayuwa mai kyau da ita, don haka muna yi wa Allah godiya muna kuma yi wa mataimakin shugaban kasa godiya da wannan damar da aka samu daga wurinsa kuma Allah ya ba mu ikon ganin ci gaban duk wanda ya samu gajiyar wannan”, inji Abubakar Musa Umar.