Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga wajen mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Dokta Sa’ad Abubakar daga fadada da ke garin Sakkwato na cewa an ga watan Azumin Ramadana a yau Lahadi don haka gibe gibe litinin za a tashi da Azumi kenan.
Bayanan da muka tattaro na cewa mai alfarma Sarkin musulmi ya sanar da hakan ne da farko a shafin twitter da aka bayar da sanarwar cewa za a yi sanarwar ganin watan kamar yadda aka saba a kafafen yada labarai na rediyo da Talbijin.
Masha Allahu Allah ya taimaka mana ayi Azumi lafiya cikin walwala da jin dadi.