Home / Lafiya / An Yi Kira Ga Iyaye Su Bayar Da Yayansu Ayi Masu Allurar Rigakafi

An Yi Kira Ga Iyaye Su Bayar Da Yayansu Ayi Masu Allurar Rigakafi

 

An yi kira ga iyaye da kuma masu kulawa ko rike yara da su tabbatar da an yi wa yarensu yan kasa da shekaru biyar allurar rigakafi.

Sanarwar ta ce kamar dai yadda Gwamnatin jihar Kaduna da kuma wadanda aka yi hadin Gwiwa da su duk sun himmatu wajen fadakar da jama’a muhimmancin Rigakafin.

 

 

Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana cewa aikin allurar Rigakafin dai zai gudana ne a tsakanin ranar 2 zuwa biyar ga watan Maris, 2024. Kuma masu aikin Rigakafin Rigakafin su bi gida gida ne da kuma kan tituna da wuraren Ibada, kasuwa da Tashoshin mota da dai sauran wurare baki daya.

A wata sanarwar hadin Gwiwa da suka fitar tsakanin babban jami’in kungiyar yan jarida masu fadakarwar game da muhimmancin yin allurar rigakafi (JAP) Lawal Dogara, da kuma hukumar kula da lafiya matakin farko ta Jihar Kaduna

Sun bayar da shawarar cewa Rigakafin za ta kare yara saboda haka iyaye su tabbatar da sun bayar da yayansu domin masu gudanar da aikin su yi aikinsu domin amfanin lafiyar al’umma.

 

Sanarwar ta yi bayanin cewa dukkan wadansu shirye shirye tuni an kammala su da nufin ganin aikin ya ta fi cikin nasara.

Sai sanarwar ta yi kira ga wadanda za su gudanar da aikin na wuccin gadi da su tabbatar sun kai ga duk inda wani yaro da ya dace ayi wa Rigakafin an yi masa kamar yadda aka tsara.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.