…za mu ciyar da mutane dari 250 a kullum
A kokarin ganin ya taimakawa al’umma domin rage radadin halin matsin da ake ciki a yau ranar daya ga watan Azumin Ramadana dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Gusau da Tsafe ya bayyana cewa “Cikin ikon Allah,yau daya ga Azumi Mun Kaddamar da raba Kayan Tallafin Abinci ga wasu daga cikin Al’ummar Gusau da Tsafe”.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Honarabul kabiru Amadu Mai Palace
da ke wakiltar mazabar Gusau da Tsafe a majalisar wakilai ta tarayya da ya rabawa manema labarai
Mun tsara bada tallafin ga Alumma daban daban da suka hada da Yan siyasa, Maaikata, Yan jarida, Yan Media, Malaman Addini, jami’an tsaro, Marayu, kungiyoyi da sauransu.
Kabiru Mai Palace ya kara da cewa “Mun yi tsarin ba Mutane kimanin 2,640 wanda za mu yi kwanaki 5 in sha Allah Muna Rabawa.
Haka mun yi tsarin rabar da dafaffen Abinchi na Mutum 250 kullum a lokachin Shan Ruwa wanda munfitar da tsarin a wasu wurare a tsakanin Gusau da tsafe duk domin mu bada gudunmuwar mu wajen rage radadin halin tsadar rayuwar da al’ummarmu Ke ciki.
Kamar ko yaushe muna bada hakuri ga Wadanda Allah bai sa sun samu ba hakuri domin ba za mu iya game kowa ba saboda game kowa sai Allah madaukakin Sarki da ya halicci kowa da komai baki daya.
Amma dai zamu yi kokari dai dai gwargwado ko yaya ne wasu su amfana ta hannun mu da ikon Allah.
In sha Allah gobe ma kamar Yau zamu ci gaba da rabawa har sai Mun kai kwanaki biyar (5)