Home / Lafiya / Tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar Kano Ya Harbu Da Cutar Korona

Tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar Kano Ya Harbu Da Cutar Korona

Imrana Abdullahi

Tsohon kwamishinan ayyuka na Jihar Kano Mu’azu Magaji, wanda Gwamna Ganduje ya sallama daga aiki ya harbu da cutar Covid – 19 da ake kira Korona bairus.

Tun a wannan lokacin dai bayanai sun nuna cewa kwamishinan ya rasa aikinsa ne bayan da ya rika nuna murna da farin cikin mutuwar tsohon shugaban ma’aikatar Fadar shugaban kasa ABBA Kyari, da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar korona.

Magaji da kansa ne ya bayyana wa duniya cewa ya kamu da cutar a shafinsa na facebook.

Kuma.kamar yadda ya ce tuni aka kai shi wata cibiyar killace wadanda suka kamu da irin wannan cuta a Jihar Kano.

Kamar yadda ya ce, “Yau da safe ne hukumar NCDC ta fitar da sakamakon Gwajin da aka yi mini kuma sakamakon ya tabbatar cewa ina dauke da cutar Covid – 19 da ake kira Korona bairus, kuma tuni aka kaini wurin da ake ajiye masu dauke da cutar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.