Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa Sanatan yankin Zamfara ta Yamma a majalisar Dattawan Najeriya Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar ( Shettiman Zamfara) shugaban kwamitin kula da harkokin ruwa a majalisar.
ya baiwa Shuwagabannin Jam’iyyar APC da Magoya bayan Jam’iyyar tare da Kungiyoyin Addinin Musulunci da kuma Kungiyoyi magoya bayan Jam’iyyar reshen jihar Zamfara Shanu guda dari uku da tamanin (380) domin gudanar da bikin karamar Sallah cikin jin dadi da walwala.
Muna rokon Allah (SWT) ya saka wannan aikin al’khairi a mizanin Mai girma Sanata Yari, Allah (SWT) ya zaunar da jihar Zamfara, al’ummarta da Arewa maso Yamma da kasa baki daya lafiya alfarmar Annabi Muhammad (SAW).