Home / Big News / Ina Nan Da Raina Ban Mutu Ba – Bala Lau

Ina Nan Da Raina Ban Mutu Ba – Bala Lau

Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Izalatul bid’a wa’ikamatus sunnah na tarayyar Nijeriya Shaihk Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa yana nan da ransa bai mutu ba kamar yadda wata kafar yada labarai ta ruwaito tana yada labarin cewa wai ya rasu kuma mutanen da duka halarci Jana’izarsa sun cadude a wuri daya ba su bayar da tazara a lokacin sallar Gawarsa Lamar yadda suka bayar da labarin karya.
A cikin wani hoton da suka wallafa a jaridarsu ta yanar Gizo sun nuna cewa Malamin ya rasu kuma mahalarta taron sun kasa bayar da tazara wajen Jana’izarsa.
A cikin wani faifan bidiyon da ya fitar lokacin da yi wa manema labarai bayani Shaikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa duk mai kokarin sai ya yada labarin karya na wani ya mutu, to ta Allah za ta iya kasancewa a kansa shi mai kokarin yada bayanin da ba haka yake ba.
“Saboda haka ni ina nan da raina ban mutu ba, kuma a yanzu ma muna shirin fara karatun Tafsirin Azumin watan Ramadana kamar yadda muka saba kuma za a yada wa jama’a masu sauraren karatun domin kowa ya amfana.
“Ina kuma yin godiya ga jama’a da suka nuna damuwarsu suka yi ta bugo waya suna tambayar halin da ake ciki”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.