Home / Big News / Gwamnatin Jihar Kano Ta Kara Dokar Hana Fita Da Sati Daya

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kara Dokar Hana Fita Da Sati Daya

 Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana batun kara dokar hana fita da sati daya.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta yi hakan ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan batun lafiya da kuma fada a ji daga bangaren Gwamnatin tarayya.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar yada labarai na Jihar kano Malam Muhammad Garba.
Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa an kara daukar matakin ne da kyakkyawar niyya domin ci gaba da yaki da annabar Covid – 19 da ake kira Korona bairus.
Ya ce an yi ne da nufin hana masu dauke da cutar shiga cikin jama’a domin dakile yaduwarta baki daya.
Sanarwar ta kuma yi kira ga daukacin jama’a cewa lokacin da suke cikin yin biyayya ga wannan dokar hana fita, ana bukatar kowa ya ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya a kokarin gwamnati na yaki da cutar.
Sai aka bukaci jama’a su ci gaba da kiyaye ka’idojin zama cikin tsafta, wanke hannu a koda yaushe, Sanya abin rufe baki da hanci tare da bayar da Tazara a duk inda ake a tsakani  jama’a.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.