Home / Labarai / Gwamna Dauda Lawal Ya Biya Tsofaffin Ma’aikata Bashin Hakkokinsu Na Barin Aiki

Gwamna Dauda Lawal Ya Biya Tsofaffin Ma’aikata Bashin Hakkokinsu Na Barin Aiki

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya biya tsofaffin ma’aikatan jihar bashin haƙƙoƙin su na barin aiki, wato Garatuti, wanda suka biyo tun na shekarar 2011, kuɗaɗen da suka haura Naira Biliyan Huɗu.
Ma’aikatan jiha da na Ƙananan Hukumomin jihar da su ka bar aiki, ba su samu haƙƙoƙin su ba na tsawon waɗannan shekaru, an tantance su an biya su.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa an biya tsofaffin ma’aikatan jihar da na Ƙananan Hukumomi waɗannan kuɗaɗe bayan tantance sahihancin su.
Ya ce, gwamnatin jihar Zamfara ta biya tsabar kuɗin da ya kai ma Naira Biliyan 4,337,087,492.06 a rukunoni huɗu na tsofaffi ma’aikatan.
Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ce, “A watan Faburairu, Gwamna Dauda Lawal ya kafa wani Kwamiti, wanda aka ɗora ma alhakin tantancewa tare da biyan tsofaffin ma’aikatan da suka bar aiki tun shekarar 2011, a ƙoƙarin sa na gyara tsarin aikin gwamnati a jihar Zamfara.
“Bayan kammala wannan tantancewar, sai ta bayyanar wa gwamnati cewa ana bin jiha da Ƙananan Hukumomi Naira Biyan 13.4.
“A biyan rukuni na farko, na biyu da na uku, an biya mutum 1,088 da aka tantance dukkan haƙƙoƙin su, inda aka biya N1,836,836,018.95
“A wannan watan, an biya mutum 284 da aka tantance kuɗaɗen su, wanda ya kai ma N499,435,942.42 a rukuni na huɗu. Hukumar Fansho ta jiha ta biya kuɗaɗen da suka kai ma N2,336,271,961.37.
“Bugu da ƙari, akwai ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da Malaman Firamare su kimanin 1,744, waɗanda suka bar aiki a tsakanin shekarun 2011 da 2018, kuma tuni an biya su haƙƙoƙin su da ya kai ma Naira Biliyan N2,000,815,530.69 a rukuni huɗu.
“Wannan biyan bashin kuɗin barin aiki, ba ƙaramin gagarumin ci gaba ba ne a wannan gwamnatin, wanda kuma babu makawa, zai kawo sauƙi ga rayuwar waɗanda suka amfana, bayan jiran tsammani na shekaru masu yawa.
“Gwamnatin Dauda Lawal ta nuna aniyar ta na jajircewa wajen cika alƙawuran da ta yi wa al’ummar jihar Zamfara.”

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.