Home / Labarai / An Samu Ci Gaba A Tsarin Dimokuradiyya – Haonarabul Balele a

An Samu Ci Gaba A Tsarin Dimokuradiyya – Haonarabul Balele a

Bashir Bello majalisar Abuja

Aminu Balele dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi a Jihar Katsina kuma dan jam’iyyar APC ya bayyana cewa babban abin jin dadin da aka samu shi ne kowa ya samu yancin kansa da kuma nasarar da aka samu ta komawa daga wata jam’iyya zuwa wata daban bayan an yi shekaru 16 a cikin karagar mulki wannan nasara ce sosai a tsarin Dimokuradiyya a canza daga wata zuwa wata ba tare da samun wata matsala ba ko kadan

” idan aka duba sosai za a ga cewa hatta jama’a ma sun samu yancin kansu ta hanyar yin zaben wadanda suke bukata domin su shugabanci su ko wakilce su , kuma Ko a karamar hukuma ne za a ga cewa akwai wakilan jama’a wato Kansiloli da jama’a za su iya zuwa gidajensu akwai kuma shugabannin kananan hukumomi duk suma suna nan tare da jama’ar gari, akwai kuma yan majalisar jiha da suma suke yi wa jama’a alkairai da dama akwai kuma Sanatoci duk wadannan jama’a na da damar yin zabensu a koda yaushe wanda sakamakon hakan kasashen duniya sun kara amincewa da Najeriya kuma ko a kasashen da ake sarauta za a ga cewa suma sun yi yar kwaskwarima a kasashen nasu ga kuma yancin fadin albarkacin baki kuma ba abin da dan Adam ke bukata kamar fadin albarkacin baki wannan babban abu ne jama’a su kara hada kawunansu.

Kunga ko a halin yanzu an samu sama da shekaru Ashirin kenan ana mulkin dimokuradiyya ko a hakan an samu ci gaba.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.