Home / Uncategorized / Za A Yi Babban Taron Tattaunawa Kan Zaman Lafiya A Jihar Kaduna 

Za A Yi Babban Taron Tattaunawa Kan Zaman Lafiya A Jihar Kaduna 

Daga Imrana Abdullahi
Karfafa Zaman lafiya da hadin kai ne Burin mu a Jihar Kaduna
A ranar Asabar ne idan Allah ua kai mu ake saran za a yi wani gagarumin taron tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umma a Jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin tarayyar Najeriya.
Shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya da ake kira a Turance ( Kaduna state peace commission) Dokta Sale Momale ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna.
Inda ya ce za a gudanar da taron yin addu’o’i a gobe Juma’a a masallatai da kuma yin addu’o’in a ranar Lahadi a Coci- Coci da ke fadin Jihar.
Kuma taron na ba na ya samu yin hadin Gwiwa tsakanin hukumar wanzar da zaman lafiya ta Jihar Kaduna da kuma a kalla kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya guda 37 da za a yi aikin hadin Gwiwar wajen ganin an cimma nasarar lamarin.
“A kalla kungiyoyi da hukumomi 37 ne suka hada Gwiwa da hukumar fadakarwa a kan samun zaman lafiya domin gudanar da wannan taron”.
Duk a kokarin da hukumar ke yi Dokta Sale Momale ya ce za a kaddamar da wadansu litattafai gida uku.
“Za a gabatar da litattafai gida uku gudunmawar matasa a
Gudunmawar mata za su bada a Jihar kaduna, Sai wani jadawalin da aka samar da al’ummar Jihar Kaduna za su yi amfani da shi domin samun zaman lafiya a Jihar kaduna,ta yadda za a samar da ingantaccen zaman lafiya a tsakanin al’umma baki daya”
Muna godiya ga Gwamnan Jihar Kaduna a kan bamu karfin Gwiwa da ayyukan da yake yi domin fadakarwar a samu zaman lafiya ba tare da nuna wani bambanci ba hakika dabi’unnan sun kara taimaka mana wajen kokarin samar da sabuwar Jihar Kaduna mai cike da albarka da dimbin tattalin arzikin kasa mai kyau da zai amfani kowa baki daya.
Dokta Sale Momale ya kuma yi addu’ar samun gama wa lafiya da kuma yin jinjina ta musamman ga Gwamnan jihar Kaduna Kwamared Sanata Uba Sani bisa irin yadda yake rungumar kowa a Jihar ba tare da nuna wani bambanci ba wanda hakan ne ya sa ake samun nasarar samun zaman lafiya a tsakanin Juna, kuma hakan na kara taimakawa ayyukan hukumar samar da zaman lafiya da dule yi”, Inji Sale Momale.
Babban taron tattaunawar a kan batun samar da zaman lafiya zai samu halartar dimbin al’umma masana a kan harkokin samar da zaman lafiya daga cikin Jihar, Najeriya da wajen ta baki daya.

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.