Home / Big News / Hakuri A Zauna Gida Ne Zai Kashe Cutar Korona – El-Rufa’i

Hakuri A Zauna Gida Ne Zai Kashe Cutar Korona – El-Rufa’i

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ya bayyana cewa hakuri a zauna a gida a matsayin abin da zai kashe cutar Korona baki daya
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan zagayen duba yadda kan iyakokin Jihar Kaduna suke, domin ganin ba a shigo da cutar Covid – 19 da ake kira da Korona bairus.
Gwamna El- Rufa’I, ya ce a koda yaushe matakan hana fitar da suke Sanya wa a Jihar ana yi ne domin kiyaye lafiyar jama’a, amma ba domin kuntatawa mutane ba.
“Nan gaba kadan da zarar an tabbatar da rahotannin samun saukin cutar ta yadda za a iya baron kowa ya ci gaba da yin abin da ya saba yi na rayuwa za a yi hakan, musamman ganin irin yadda Gwamnati ke duba yanayin yadda cutar take a koda yaushe”.
Ya ci gaba da cewa suna yin aiki kan jiki kan karfi ne domin ganin cutar bata yadu ba kuma za a tabbatar da ganin wasu mutane ba su shigo da cutar daga wasu wurare da ba Jihar Kaduna ba.
“Nan gaba kadan komai zai kwaranye cikin ikon Allah kowa zai koma kan irin abin da saba domin gudanar da rayuwarsa”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.