Sakon Samaila Baki…
Me Rabon Duka Bai Jin Bari…
Kwanakin baya nayi matashiya a kan yadda kananan yara, yan bakwaini ke cin mutuncin yayyen su da kuma dattawa wadda sun isa su haife su, ko kuma suna da irin su a gida.
So tari, zaka ga bakwainin nan a kafafen sada zumunta ta zamani suna cin zarafin mutane ba tare da hujja kwakkwara ba. Sai dai kawai suta sakin layi suna kazafi, batanci da karanbani da kuma nuna jahilci akan abin da basu sani ba. Wannan abin kan daura man kai inta tunani da nadama, ganin irin wannan harkar.
In kayi masu nasiha, sai su ci zarafin ka, suyi maka kachakacha wai suna da yancin fada albarkacin bakka. Kazafi da sharri, karya da cin mutuncin mutane ba yancin fada da albarkacin baka ne ba. Yancin fada albarkacin bakka, shine ne kayi magana a kan tsari da kuma hujja ba kawai karya ko batan ci ba.
Indai matashi ya ce zai cigaba da sharri, da kuma karya da reni, to gaskiya ba tarbiya bane kuma lahanni ne babba, har wa yau, zai iske kansa cikin yanayi na matsatsi domin; dayawa daga cikin wanda aka saba masu, zasu nemi hakinsu a kotu.
Daga karshe, zanyi anfani da wannan damar, in jinjina wa da yawwa daga cikin matasan mu wadda suke kwantata tarbiya da kuma sanin yakamata a duk alamuran su.
Muna alfahari da rukunin wayyanan matasan, domin sun ciri tuta kuma abin jinjina masu ne. Sun zama abin koyi da kuma adon gari, a matsayin su na mutane masu kwatanta tarbiya, kawaici da dadtaku. Muna masu fatan alkhairi, kuma Allah ya tabbatar masu da duk buri na alkhairi duniya da lahira.
Dan Allah mai rabon duka baya jin bari.
Sama’ila Baki ne ya rubuta shi.