Home / MUKALA / An Yi Karamar Sallah A Cikin Yanayin Ba Sabun Ba

An Yi Karamar Sallah A Cikin Yanayin Ba Sabun Ba

 Mustapha Imrana Abdullahi ne ya rubuta wannan
Sabanin irin yadda aka saba yin bikin murnar karamar Sallah bayan kammala Azumin watan Ramadana, musamman a tarayyar Nijeriya an yi bikin ne a cikin wani yanayin da za a iya kiransa da mawuyacin hali kasancewar a wasu jihohi irin Kaduna ko taron yin Sallar Idi da aka saba a manyan filaye ba samu yi ba kasancewa Gwamnatin Jihar ta haramta taron jama’a sai dai kowa ya yi a gidansa tare da iyalansa, kuma bisa ka’idojin Sanya Takunkumi, bayar da Tazara tsakanin Juna tare da wanke hannu ba kuma batun yin musabisa da aka Sani a addinin Islama ana samun lada ne idan mutane suka hadu.
Kuma a bisa dukkan bayanan da muke samu a Jihar Kaduna musamman a manya manyan garuruwan da suka hada da cikin babban birnin Jihar wato Kaduna da ya hada kananan hukumomi hudu saboda kananan hukumomin Igabi da Chikun akwai wadansu muhimman bangarorinsu duk suna cikin garin  na Kaduna, ba a samu inda aka ce an yi Sallar Idi ba sai dai wai ta yan magana gari da yawa maye bayacin kansa wato akwai wadansu garuruwan na cikin Lunguna a yankunan karkara wanda su tun asali ma ba su san ana Dokar dakile Korona ba domin a bisa binciken da muka yi ba su ma san da wani ABU cutar Korona ba don haka mafi akasarinsu har yanzu ba su ma san da cutar ba, to, a irin wadannan wurare idan an samu rahoton yin Sallar Idi babu mamaki.
Da muka zagaya cikin garin kaduna da wasu wurare a kauyuka mun ga irin yadda mutane ke zama a rukuni rukuni suna ta hirarsu kasancewa akwai dokar hana fita kuma da yawa mutane ba su da abin hawa don haka tun da ba abubuwan hawa na haya da za su sa kudinsu a kai su inda ake so sun hakura, wadansu ma ko Dinkin Sallar ma babu kamar yadda mafi yawa suka hakura da yin tuwon Sallah sakamakon ba yadda za a yi, sai dai a rika ba yara irin tuwon makwabta idan an kawo masu.
Teloli: haka abin yake a wajen batun dinkin sutura ma wasu ba su samu yin Dinkin ba domin babu wasu kuma suna tsoron kamuwa da  cutar Korona bairus don haka ba su kai Dinkin ba ma domin ba su san waye zai kawo nasa dinkin kamar su ba domin gudun rashin dace a samu wani bai ma san yana da cutar ba ya kuma kawo nasa Dinkin.
Duk wannan kuncin dai ana ganin ya faru ne sakamakon matsalar cutar Covid – 19 da ake kira Korona bairus da ta haddasa a duniya baki daya.
Koda yake masu iya magana na cewa Allah daya Gari bamban a wasu Jihohin mun gani a kafar yada labarai ta Talbijin Gwamnoni da kansu sun halarci filin da aka yi Sallar Idin inda aka ga Gwamna Ganduje ya Sanya takunkumin rufe baki da hanci tare da bayar da Tazara.
Lamarin dai a Jihar Katsina kamar yadda wakilinmu ya tuntubi wadansu mutane sun bayyana cewa hakika sun yi Sallar Idi tare da samun wata tangarda ba, har ma wakilinmu ya gani a kafar Talbijin a cikin garin Katsina an yi Salllar tare da bayar da Tazara, har wadanda aka yi hira da su suke yin kira ga Gwamnati ta kawo karshen yawan kashe kashe da kai hare hare tare da satar mutane domin neman kudin fansa, saboda kamar yadda suka bayyana lamarin ya addabi jama’a.
Kuma an ji shi yana kira ga jama’a da su ci gaba da kiyaye doka da ka’idojin yaki da cutar Covid -19 da ake kira Korona bairus, ya ce a lokacin yin Sallar Idi da kuma dukkan ma’amalolin da za a yi baki daya.
Shugaba Muhammadu Buhari, shima shugaban tarayyar Nijeriya wakilinmu ya Ganshi a cikin hoto tare da iyalansa kawai suna sallar Idin karamar Sallar ta bama, ko irin Jikokin nan nasa da sukanzo ba a gani ba, domin daman ya fitar da sanarwa cewa zai yi Sallarsa da iyalinsa a gida ne kawai don haka kowa ya yi tasa Sallar a gida.
Dangantaka tsakanin Ma’aurata, hakika halin da aka shiga na zama a gida saboda cutar Korona bairus ya haifar da dimbin matsaloli tsakanin ma’aurata maza da mata saboda wadansu lamarin ya haifar masu da lalacewar aure wasu kuma ana zaman doya da manja a tsakaninsu Lamar yadda na gani da idanuna tsakanin makwabcinmu da iyalinsa.
Batun Yawon Sallah, To batun yawon Sallah dai a halin yanayin dokar zama a gida abune mai wahala yara suje Mesa sai dai a cikin unguwanni, ko kuma ranakun da ake sassauta dokar hana fita kawai.
Dama abin da wadansu Gwamnoni Gwamnoni musamman masu tsananta dokar hana fita domin kiyayewa kada a kamu da cutar Korona shi ne a cikin unguwanni kamar yadda muka ambata a baya cikin wannan rubutu cewa kamar a kauyuka ba san da cutar ba ma Sam domin a cikin unguwanni masu sa Takunkumi sai daidai kawai haka batun yin tazara nan ma ba sosai ba, jama’a na ta yin harkokinsu kawai ba tare da shayi ko shakkar komai ba.
Gaishe Gaishe, akwai wata al’ada ta shiga cikin gidaje musamman ranar Sallah da magidanta kan yi a ranar Sallah suna gaida mutanen cikin gidan bayan an sauko daga Sallar Idin karama ko babbar Sallah, wannan ma ya zama sai nadiran kawai a wurare da dama.
Mustapha Imrana Abdullahi ne ya rubuta wannan Makala, za a iya samunsa a lamba kamar haka 080 3606 5909.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.