….Bamu amince da sallamar ma’aikata ba sai an ba su hakkokinsu
Kwamared Ado Gaya mataimakin shugaba ne na kungiyar ma’aikatan hukumar wutar lantarki na shiyyar Arewa ya shaidawa manema labarai cewa sun shiga yajin aiki ne sakamakon irin kokarin da mahukuntan Kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Kaduna ke yi domin korar ma’aikatan kamfanin a shiyyar su dari Tara, (900).
Kwamared Ado Gaya ya ci gaba da bayani ga manema labarai a harabar bakin shiga Kamfanin cewa su ba su amince da wannan tsarin ba sai dai a bi dokar daukar ma’aikata idan za a Kori ma’aikaci a ba shi duk wadansu hakkokinsa kamar yadda dokar ta tanadar.
“Akwai da matsaloli da yawa da suka hada da batun rashin kulawa da lafiyar ma’aikata da dai sauran tanaje tanaje da dama duk da suna nan a cikin kundin tsarin mulki amma a wannan kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kaduna ba a kula wa da su. Shiyyar Kaduna dai ta hada da Jihohin Sakkwato, Zamfara,Kebbi da kuma Kaduna kanta”.
Kwamared Ado Gaya ya kuma shaidawa manema labarai cewa kamar yadda aka ga sun kashe wutar lantarki a Kaduna tun daga hedikwata duk a ko’ina ma babu wuta duk sauran Jihohin baki daya sun kashe wuta har sai an kula da hakkokinsu kamar yadda dokar aikin ta tanadar.
Da wakilin mu ya ziyarci harabar ofishin rarraba wutar lantarki na Kaduna ya ga irin yadda dukkan ma’aikatan Maza da mata suka fita baki dayansu a waje suna Zanga zangar yajin aiki.
Idan mun samu zantawa da jami’an kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Kaduna da ake kira Kaduna electric, zamu kawo maku bangaren na su bayanin.