….Auwal Yaro Mai Kyau ya zama abin ko yi
A kokarin ganin al’umma sun samu damar zama da kafafunsu bayan sun samu ingantaccen ilimi tun daga matakin farko a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya ya sa dan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi a karamar hukumar Kaduna ta Kudu Honarabul Auwal Yahaya da ake yi wa lakabi da Yaro mai kyau, ya h8mmatu wajen biyawa marayu da sauran marasa galihu da ke cikin al’umma kudin rubuta jarabawar fita makarantar Sakandare domin su samu damar ci gaba da yin karatunsu.
Da suke gabatar da jawabansu a wajen taron tabbatarwa da kuma shaidar gabatar da daliban da za su rubuta jarabawar fita Sakandare ta NECO da aka yi taron a makarantar Aunt Nicas a cikin Tudun wada Kaduna
Umar Yahaya, mai taimakawa dan majalisar Jiha mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi, hakika wannan aikin wani bangare ne da yake yi a kowace shekara ya biyawa yara dalibai kudin makarantar jarabawar fita Sakandare ta WAEC ko NECO don haka ne ma a yau muke yin taron biyawa dalibai a kalla 50 kudin jarabawar NECO.
Wannan dan majalisa a koda yaushe ya na son taimakawa mutane musamman ma wadanda suka kasance marayu da marasa galihu kuma wadannan ku ne da kuka yi sa’a kasancewar akwai mutane dayawa da suke bukatar a ba su wannan damar don haka muke yin kira ga dalibai marayu da sauran marasa galihun da suka halarta da su yi kokarin cin jarabawar da za su rubuta.
Malam Mustapha na jam’iyyar APC a mazaba ta Goma sha daya (11), a karamar hukumar Kaduna ta Kudu, dan majalisa Auwalu Yaro Mai kyau wannan shi ne karo na hudu da dan majalisar ke biyawa dalibai kudin jarabawar NECO da duk shekara ana samun kari ne na yawan daliban da ake biyawa kudin jarabawar.
Tarihin dai wannan a wannan makaranta ta Aunt Nicas da ke cikin unguwar Tudun Wada Sabon gari Kaduna.suma suna da tsari ne na biyawa dalibai marayu suna taimaka masu tun da suka zo wajen dan majalisa sai kawai faduwa tazo dai dai da zama.
“Muna rokon Allah ya ci gaba da Tallafawa irin wannan harka ta ci gaban ilimi musamman na marayu da sauran marasa galihu”.
Wadansu ayyuka da yake yi akwai dakin duba marasa tafiya a matakin farko muna da akalla guda hudu a wannan mazaba hakika ya yi kokari a gwamnatacce an kawo masu kayan aiki dukkansu, amma a matsayinsa na dan majalisa ko a kwanan nan sai da mutanen mazabar Sabon gari suka zo da korafin ba makewayi wanda a halin yanzu.
Akwai kuma dalibai na makarantar kiwon lafiya ta Halim da suke Koyar da kiwon lafiya kuma a halin yanzu kwalliya na biyan kudin sabulu wanda a halin yanzu ma har wata dalibar ma na aiki a asibiti duk domin kokari da kwazo irin na dan majalisa.
Dan masanin Sabon gari, Dokta Suleiman Muhammad, hakika muna karfafa wa dan majalisa Gwiwa a bisa irin ayyukan ci gaban jama’a da yake yi musamman a bangaren ilimi.
Domin saboda talauci da gazawa sai kaga dalibai na samun kazawa a fannin biyan kudin jarabawa.
” A matsayin dan majalisa aikinsa shi ne yin doka ya kuma tabbatar Gwamnati ta yi abin da ya dace ta yi wa jama’a kuma a madadin al’umma baki daya muna yi wa dan majalisa godiya. Muna yin kira ga wannan makaranta da su yi kokarin taimakawa wannan dalibai a kan yaddabza su rubuta jarabawar da aka biya masu domin idan dalibi na son nasara dole ne ya samu a kalla darussa biyar da zai ba su damar su samu nasarar wucewa gaba bayan an samu lashe jarabawar darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi da zai ba dalibai damar wucewa gaba zuwa makarantun gaba da sakandare”.
Dokta Suleiman ya kuma yi wa daliban alkawarin cewa zai taimaka masu wajen samun damar shiga makarantar gaba da Sakandare.
“A duniya fa a yanzu Najeriya ce ke kan gaba wajen yaran da ba su zuwa makaranta kuma a Najeriyar ma arewacin a kan gaba da ake samun yara marasa zuwa makaranta don haka ya dace ayi abin da ya dace. Ba fa batun ya rika zuwa ga jama’a ya na raba masu kudi ba ne a’a ilimi ne kashin bayan ci gaban komai na ci gaban al’umma duk wanda ya je sama ya sa hannu ya jawo na bayansa”.
Muna yin kira ga yan siyasa baki daya da su ma su tashi tsaye wajen yin irin wannan aikin ga jama’a.
Datktan makarantar Halilu Abdul da aka fi Sani da Mista Kayode, hakika wannan aikin da dan majalisa Auwal Yaro ke yi shi ne na rage talauci da sauran ayyukan batagari a cikin al’umma kamar yadda Auwalu ya yi mana alkawari kunga ya cika yazo ya ce zai biyawa dalibai 50 kirin jarabawar NECO kuma ya cika kamar yadda kowa ke gani.
Ga dalibai ya dace kuba marasa kunya ta hanyar yin kwazon cin jarabawa haka kuma muna yin kira ga dalibai da iyayensu da a koda yaushe a rika barin dalibai suzo a Koyar da su yadda za su iya cin jarabawa.
Abubakar Abdulkadir layin Faki a cikin garin Kaduna, hakika wannan dan majalisa ya ta ba zuciyar al’umma domin ba abin da zai taimaki mutum kamar ilimi domin mainilimi ne ke daukaka.
“An yi jagorori da yawa a baya amma ba a yi kamar wannan ba da wannan dan majalisar ke aiwatarwa na ci gaban al’umma baki daya, muna yin addu’ar Allah yasaka wa masu ba dan majalisa shawara.
Honarabul Abubakar Umar Tunau, wannan dan majalisa ba yau baya fara ba domin daman aikinsa ne na taimakawa marasa galihu da mabukata a cikin jama’a.
Ya kuma yi kira ga dalibai da su yi aiki da abin da suka koya a makaranta a cikin al’umma
Ya bayar da shawarar cewa ya dace a rika kokarin samun mata a matsayin Likitoci ta yadda suma za su taimakawa mata a lokacin rashin lafiya a rika yin aiki da al’amarin koyarwar addinin Islama.
Dalibai su kiyaye domin gujewa jin kunyar samun satar jarabawa wanda idan an ke gaba sai a samu matsala
Sarkin Kwarin Sabon Garin Tudun Wada Auwal Usman Matawalle, bayar da misali ya yi cewa ko a shekarun baya lokacin muna yara akwai wanda ya kasa rubuta jarabawa saboda rashin kudi naira dubu daya na biyan kudin
Shugaban Masallatan Juma’a na yankin mazabar Unguwar Sanusi da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu kira ya yi shima ga dalibai da kada su ba jama’a kunya don haka su yi kokarin rubuta jarabawa da kansu ba tare da wani ko wasu sun rubuta masu jarabawar ba.
Sai ya yi kira ga dalibai cewa lallai ya fitar da kowa kunya domin wadanda suka rubuta suna bukatar wannan a biya masu kudin jarabawa sun fi dubu amma aka tantance har aka samo dalibai dari da Saba’in 170 da aka biya wa kudin jarabawar WAEC da NECO.
A kwanan baya ne aka shirya wani gagarumin taron yin murnar daukar nauyin biyawa yara kudin jarabawar WAEC su dari da Ashirin da suke karatu a makarantar kwalejin Shaikh Abubakar Gumi da ke Tudun Wada Kaduna.

An kuma fadakar da al’ummar duniya irin yadda dan majalisar ke yin kokari a fannoni daban daban tun daga samawa matasa ayyuka da dai kulawa da dimbin al’amuran da za su taimakawa rayuwar jama’a da dama.
Kamar yadda muka samu labari sakamakon irin wadannan ayyukan alkairi na biyawa marasa galihu kudin makaranta musamman na jarabawar Sakandare da wadansu da yawa basa iya biyawa yayansu a halin yanzu ma wadansu yan majalisa abokan sa suma an yi masu kaimin tashi tsaye sun fara yin ko yi da abin da Auwalu Yaro Mai kyau ke aiwatarwa a mazabarsa.