Related Articles
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bayyana sunan Furofesa Kabir Bala, a matsayin sabon mataimakin shugaban jami’ar.
Kafin Nadin nasa dai Furofesa Kabir Bala mataimakin shugaban jami’ar ne mai kula da harkokin mulki a makarantar.
Nadin nasa dai zai fara aiki ne a ranar 1, ga watan Mayu, 2020. Muna fatan Allah ya taya riko.