Home / Labarai / Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Karrama Fitattun Yan Nijeriya

Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Karrama Fitattun Yan Nijeriya

A wannan hoton ana iya ganin tsofaffin Gwamnonin Jihohin Neja Aliyu Babangida da na Kaduna da kuma Gwamnan Neja mai ci sai Yariman zazzau
A wannan hoton ana iya ganin Gwamnan Jihar Neja Abubakar sani Bello a tsaye da fararen kaya sai tsofaffin Gwamnonin Neja Aliyu Babangida da na kaduna Alhaji Dakta Muktar Ramalan Yero sai kuma Alhaji Mannir Yariman Zazzau da kuma jami’an gidauniyar tunawa da sardauna Ahmadu Bello

Daga Imrana Abdullahi

A kokarin da gidauniyar tunawa da marigayi Sa, Ahmadu Bello sardaunan Sakkwato keyi domin kara karfafa wa daukacin al’ummar yankin arewa da kasar baki daya na su ci gaba da aiwatar da aikin ciyar da kasar baki daya gaba yasa gidauniyar ta Karrama wadansu fitattun kasar guda hudu da suka hada da tsohon shugaban Nijeriya Yakubu Gawon, Mai shari’a Hajiya Fati Abdussalamu Abubakar, Marigayi tsohon shugaban Nijeriya Alhaji Shehu Usman Aliyu shagari da Marigayi mista Sunday Awoniyu Visa la’akari da kwazon ayyukan da suka yi na ciyar da kasar gaba.

A dama tsohon shugaban Nijeriya Alhaji Abdussalamu Abubakar ke mikawa tsohon shugaban kasa Yakubu Gawon lambar girmamawa da gidauniyar tunawa da sardauna ta bashi wanda Lutanar janar mai ritaya Abdurrahaman Dambazau ya karba a madadinsa

A dama tsohon shugaban Nijeriya Alhaji Abdussalam Abubakar ne ke mikawa tsohon shugaban kasa Yakubu Gawon babbar lambar karramawa da lutanar Janar mai ritaya Abdulrahman Dambazau ya karba a madadinsa da gidauniyar tunawa da sardauna ta bashi.

Shima shehu shagari
A dama tsohon Gwamnan Jihar Neja Aliyu Babangida ne ke mikawa tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari lambar girmamawa da gidauniyar tunawa da marigayi Sardaunan ta bashi.
Shima Sunday Awoniyi
A wannan hoton za a iya ganin Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello yana mikawa marigayi Sunday Awoniyi lambar karramawa da gidauniyar tunawa da Sardauna ta bashi sakamakon aikin ci gaban kasa da ya yi a lokacin rayuwarsa.

A wannan hoton za a iya ganin mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu yana mikawa uwargidan tsohon shugaban kasa Abdussalamu Abubakar mai shari’a Hajiya Fati Lami Abdussalamu Abubakar lamabar karramawa saboda aiki tukuru da take yi wa kasa.
A wannan
A wannan hoton ana iya ganin Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello da fararen kaya suna gaisawa da tsohon Gwamnan Neja Alhaji Dakta Aliyu Babangida shugaban kwamitin amintattun gidauniyar tunawa da Sardauna Gamji Kazan kwarai a wajen babban taron da aka yi a Kaduna

Ku ci gaba da bibiyarmu a www.theshieldg.com mujallar titanic domin kawo maku Karin wadansu hotunan nan gaba, domin ku ga yadda babban taron ya gudana.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.