Home / Uncategorized / A Kafa Dokar Ta Baci A Jihar Zamfara – Dokta Suleiman 

A Kafa Dokar Ta Baci A Jihar Zamfara – Dokta Suleiman 

 

Sakamakon irin yadda al’amura da kuma harkokin tsaro suke kara shiga cikin wani mawuyacin hali inda ake samun salwantar rayuka da dukiyar jama’a a jihar Zamfara ya sa wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama  Dokta  Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya yi kira a wani taron manema labarai a Kaduna cewa a kafa dokar ta baci a jihar.
Dokta Suleiman Shinlafi ya yi wannan kiran ne a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna, inda ya yi kira ga dhugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa ya dace ya duba yanayin da talakawan da sika zabe shi da gagarumin rinjaye suke ciki a Jihar Zamfara da suke cikin kakanikayi da har suke rasa rayukansu da dukiya.
“In fa ba a kafa dokar ta baci a Zamfara ba za a wayi gari shugaban kasa ya rasa rinjayen da yake da shi a Jihar Zamfara, kasancewar jihar Zamfara a matsayin jihar da shugaba Tinubu ya lashe zabe da gagarumin rinjaye wanda ya samu nasarar darewa a kan karagar mulkin Najeriya a matsayin hamshakiyar kasa a Nahiyar Afitka da duniya baki daya”.
Dokta Shinkafi ya kara da cewa a kwanan nan fa aka samu wadansu makiya Allah da suka yi wa Talakawan da suka sace a karamar hukumar Kauran Namoda aka yi wa wadansu mutane Maza da Mata har da yara kanana aka yi masu yankar Rago bayan kama su da yan bindiga suka  yi duk da sun karbi kudin fansa a kalla naira miliyan Talatin daga yan uwan wadanda aka kama da suka sayar da Gonaki da wadansu kaddarorin da suka mallaka amma aka yi wa wadan da aka kama yankan rago kamar yadda lamarin ya bayyana a cikin wani faifan bidiyon da ya bayyana.
” Muna son a kafa dokar ta baci a Jihar Zamfara a samar da wata gwamnati karkashin Soja idan Al’amuran tsaro sun  inganta sai a mayar wa wanda ke yi ya karasa lokacin da aka zabe shi kawai, amma idan ba haka ba lallai sai an nemi masu zabe da za su yi zabe a ranar zabe mai zuwa a jihar Zamfara ba za a samu ba domin kowa ya tsere domin tsira da rayuwarsa da lafiyarsa, wasu kuma a halin yanzu ma duk an kashe su kowa ya san hakan lamarin yake “.
Shinkafi, ya ci gaba da bayanin cewa ya na son ya sanar da Gwamna Dauda Lawal cewa lallai za su kai shi kara a gaban kotun duniya a saboda matsalar da ta afku na yi wa mutane wasu Mata da yara 38 yan kan Rago bayan yan ta’adda sun karbi naira miliyan Talatin na kudi daga yan uwan wadanda suka kama.
” Muna kuma yin kira ga Gwamnan Zamfara da ya dawo da hankalinsa ya zauna da ministan tsaro domin su hada kai a lalubo hanyar warware wannan matsala da take addabar jama’a baki daya ta tsaro, kasancewar a yanzu sukkan kananan hukumomin da ake da su guda 13 cikin jihar Zamfara duk yan ta’adda ne ke yin abin da suka ga dama, in banda babban birnin Jihar wato garin Gusau wanda shima an fara samun wasu yan ta’adda na shiga suka yin aika aika a wurin”.

About andiya

Check Also

10,000 South East Pupils Get School Bags From Collins Onyeaji Foundation

    No fewer than 10,000 pupils in the South East Zone of Nigeria are …

Leave a Reply

Your email address will not be published.