Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Bashir Nafaru tsohon Dan takarar majalisar Talatar Mafara da Anka ya bayyana abin da Ake yi a Jihar Zamfara a matsayin abin ban haushi da ban takaici domin mu muna fatar a tsaya ayi wa kowa adalci a dubi cancanta don ya yi takarar Wanda ya cancanta a cikin kowace jam’iyya ce Bashi takarar ya yi takarar shugaban karamar hukuma KO Dan majalisar jihar KO tarayya a duba Wanda ya wahala a cikin jam’iyya.
“Saboda idan kun duba duk wadanda suka yi Wanka Babu wani da ya kasance Dan tsohuwar PDP tun daga bakin wancan Kurya har wannan Maharazu Faruwa Babu Wanda za a ce Shi ne Dan tsohuwar jam’iyya inda ya Bari yaje Neman Kudi wannan abin takaici ne Babu kishi na ci gaba a gare mu don haka abin takaici ne kawai koda yaushe kawai ace sune kuma duk yadda kake son ace Kai ne sai an wayi gari ba Kai ne ba don haka idan za mu yi siyasa mu daure mu yi siyasa wadda take mun yi gadonta a kasar mu, yanzu KO a lokacin Sardauna duk alkairin da Yake yi akwai Wanda KO hanyar ba ya bi inda Sardauna ya bi ha irinsu marigayi Aminu Kano da kowa ya San Dan adawa ne sannan Bai son komi a gareka sannan kuma saboda yin adalci da kishin talaka da Yake yi mutane ke son Shi din haka a Jihar Zamfara siyasa ta rigaya ta lalalce kowa abin da Yake duba wa yaya za a yi ya samu duk arzikin Abdul’aziz Yari sai gashi an Kada Shi ya koma Bai da KO kansila tun nan ya dace mutanen Zamfara mu San abin da muke yi mu San abin da muke yi, Allah na iya Baka girma Baka da KO Sisi kuma Allah na iya Baka Kudi Baka da ilimi don haka muyi amfani da damar da Allah ya ba mu mu marasa.
THESHIELD Garkuwa