Home / News / Gamayyar Kungiyoyin Fulani Sun Koka Bisa Kisan Mutane 85 A Kudancin Kaduna

Gamayyar Kungiyoyin Fulani Sun Koka Bisa Kisan Mutane 85 A Kudancin Kaduna

Gamayyar kungiyoyin Fulani guda biyar reshen Jihar Kaduna a arewacin tarayyar Nijeriya sun koka game da irin yadda ba gaira ba dalili wadansu mutane da ba su son zaman lafiya suka kashe masu mutane 85 a hargitsin da ya faru a kwanaki uku da suka gabata.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne a lokacin wani taron manema labarai da suka kira a Kaduna.

Alhaji Haruna Usman Tugga, wanda ya yi wa manema Labaran bayani da harshen Hausa ya koka a kan irin yadda shugabannin gargajiya a Kudancin Kaduna suka koma ba ruwansu da wata kabila sai wadda suka fito cikinta kawai.

Haruna Tugga ya ci gaba da cewa hakika irin abin da yake faruwa a yankin Kudancin Kaduna abin mamaki ne kwarai matuka, saboda masu shugabancin al’umma na gargajiya babu abin da ya shafe su da wani ko wadansu kabilu sai wadanda suka fito a cikinsu kawai.

“Amma abin ba haka yake a kasar Zazzau ba domin shi mai martaba Sarkin Zazzau da masarautarsa suka kare yanci da mutuncin dukkan mutumin da yake zaune a wannan masarauta ba tare da la’akari da yanki ko kabilar da ya fito ba ko ma addinin da mutum yake yi ana kare masa yancinsa ne kawai baki daya”.
Gamayyar kungiyoyin sun hada da kungiyar MACBAN, bisa jagorancin Alhaji Haruna Usman Tugga, sai kungiyar GAFDAN, karkashin Ardo Idris Gundaru, sai kuma Barista Nuhu Ibrahim da yazo karkashin jagorancin MOFDA, Alhaji Abbas J. Julde, shugaban BAFYAN reshen Jihar Kaduna da kuma kodinetan kungiyar FUDECO karkashin Barista Abubakar Ibrahim Naseh, duk sun bayyana irin bacin ransu da abin da ya faru ga Mutanensu ba gaira ba dalili.

“Abin da ya faru a Zangon Kataf rikici ne da ya faru tsakanin Bahaushe da Bakatafe a kan Gona me ya shafi Bafilatani da yake a kauye, wanda har ana neman mutane dari da Talatin (130) ba a san inda suke ba domin sun Baro wurin da suke ada ana magana da su amma daga baya sai aka ji su shuru, banda mutane 85 da aka rufe Gawarsu an kashe su haka kawai.

“Mu shi yasa muke ganin wannan abin shiryayye ne addini da kabilanci kawai ake yi mawa”.
Ya kara da cewa ” Mu muna zargin Katafawa ne domin sune suka aikata wannan aikin bisa ingantattun hujjojin da muke da su a fili”.

Kuma an fara yin wannan abin ne a ranar 11 ga wannan watan da muke ciki.

Haruna Tugga ya bayyana cewa mafita a kan wannan lamari shi ne a kamo wadanda suka aikata wannan abin domin a tabbatar masu da adalcin abin da suka aikata.
Muna kiran jama’armu da su yi hakuri kada wanda ya dauki doka a hannunsa a zurawa Gwamnati idanu da sauran dukkan hukumomi baki daya muga irin matakan da za su dauka.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.