Home / Labarai / An Nada Matar Gwamnan Bauchi Sarauniyar Bauchi

An Nada Matar Gwamnan Bauchi Sarauniyar Bauchi

Imrana Abdullahi
Mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Dokta Rilwanu Suleiman Adamu, ya ba wa Uwargidan Gwamna Bala Mohammed Sarautar Sarauniyar Bauchi.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani sakon da Ajiyan Bauchi da Babban Limamin Bauchi suka idda sako daga fadar Mai Martaba.
A wannan hoton za a iya ganin Gwamnan Jihar Bauchi tare da Matarsa lokacin da aka kawo sakon sarautar da aka ba matar Gwamnan.
Saboda wannan karamci shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Bauchi ya fitar da sanarwa ta shafinsa na facebook, yana cewa “Muna godiya. Allah ya kara wa Sarki daraja. Amin

About andiya

Check Also

TINUBU YA NADA GEORGE AKUME A MATSAYIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYA

Daga Imrana Abdullahi Kamar dai yadda jaridar “Vanguard” ta rawaito cewa tun bayan rantsar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.