Home / Big News / KASTLEA Sun Karyata Batun Kama Keke Napep 800 A Kaduna

KASTLEA Sun Karyata Batun Kama Keke Napep 800 A Kaduna

 Imrana Abdullahi
Shugaban Hukumar tabbatar da yin biyayya tare da kiyaye dokokin hanya na Jihar Kaduna Mejo Garba Yahaya Rimi, Mai murabus, ya musanta bayanan da wasu ke yadawa cewa wai sun kama Babura masu kafa uku da aka fi Sani da (Keke Napep) sama da Dari 800.

Garba Yahaya Rimi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
“Ni iya abin da na Sani shi ne ma’aikatan hukumar da nake yi wa jagoranci sun samu nasarar kama Babura masu kafa uku Dari shida ne da wani ABU amma ba kamar yadda wasu ke yadawa ba wai an kama sama da dari Takwas, hakika wannan ba gaskiya bane”.
Ya ci gaba da bayanin cewa an kama wadannan Babura masu kafa uku ne a sakamakon laifuka daban daban na karya dokokin tukin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa, wanda kowa ya sansu domin ba boyayyen al’amari bane.
Tun a lokacin da aka fara sanyawa masu haya da Babura mai kafa uku ka’idar daukar jama’a, na su dauki mutane biyu domin tabbatar da yaki da annobar cutar Korona, an samu basa bin wannan ka’ida wanda sakamakon hakan aka Sanya dokar hana yin haya da Baburan baki daya, a bisa haka ne duk wanda aka kama yana haya, to, shimla ya san abin da zai same shi daga nan.
A game da batun mayarwa da masu Baburan abubuwansu kuwa idan Gwamnati ta bayar da umarnin hakan, Garba Yahaya Rimi, ya ce sai sun tabbatar da cewa lallai na mutum ne bayan an tantance takardun baki daya.
An dai yi kira ga jama’a da su daina yada karya a kan abin da ba su san shi ba domin hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.