Home / Big News / An Kakkatsa Al’ummar Musulmi – Shaikh Yusuf Sambo Rigacikun

An Kakkatsa Al’ummar Musulmi – Shaikh Yusuf Sambo Rigacikun

Daga Imrana Abdullahi
…hadin kan al’ummar Musulmi wajibi ne
An bayyana irin yadda aka Kakkatsa Al’ummar Musulmi da cewa shi ne babban dalilin da ya sa kasar Isra’ila ke wugiggiga Musulmi a duk fadin duniya.
Idan Su Isra’ila da kasar Amurka sun kammala da waccan kasar Musulmi sai wata kuma kasar ta Musulmi za su shiga su kuma yake ta, saboda su ba su san dan shi’a ba, ba su san dan Izala ko dan darika ko wata kungiyar Musulunci ba, su dai kawai Musulmi kawai suke haka illa iyaka.
Shaikh Yusuf Sambo Rigacikun ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake gabatar da Tafsirin watan Azumin Ramadana na Bana da aka yi a Masallacin tunawa da marigayi Shaikh Muhammadu Abubakar Gumi da ke unguwar Rigachikun Kaduna arewacin tarayyar Najeriya.
Idan ana son zaman lafiya a girmama shugabanci, shugaba dai na da karfi ne kashi dari bisa dari,  idan ana son zaman lafiya sai shugaba ya rike kashi arba’in na karfisa kashi Sittin kuma aba wadanda ke tare da wannan shugaban domin yin aiki na gaskiya da adalci daga an zo yin wani al’amarin da zai cutar da shugaban zai iya tare wa da kashi arba’in din nan haka suma idan an bi ta wajen su za su iya kare wa da karfin  kashi Sittin din nan da ke hannunsu.
Kuma idan kuna don al’amuran ku su ta fi da kyau to, ku girmama shugabancin shugabanninku.
“Ku rika tausasa murya wajen kiran sunan Annabi Muhammadu S A E, kada ku daga murya wajen kiransa.
Sai ya jawo hankalin al’ummar Musulmi da su rika yin hakuri da juna kamar yadda Alkur’ani ya haɗa mu,Sunna ta haɗa mu, Allah ya haɗa mu ne domin mu zauna tare kamar yadda kowa ya kasance akwai Musulmi,Kirista da ma wadanda ba su da addini kuma ba wanda zai iya korar wani a cikin kasar
Ya kuma yi kira ga shugaban kasa da ya yi wa shugabannin tsarin Najeriya ya yi masu jan ido ya ba su watanni uku kawai ya ce lallai su magance matsalar tsaro a Najeriya domin zubar da jinin da ake yi ya yi yawa.
Kasancewar arewa na da yan majalisar ƙasa da na dattawa don Allah ki daina zama mutane da Bebaye a rika yin wadansu ayyukan a wadansu yankuna amma ba arewa, kuji tsoron Allah ku rika magana a game da ci gaban yankin arewa, ina maganar ayyukan wutar Kabila, jawo ruwan teku zuwa arewacin Najeriya da sauran muhimman ayyukan da aka fara tun a lokacin marigayi shugaba Muhammadu Buhari
“Bani wata fa’idar a rika yin cece- kuce a kan batun Tuhajjudi, hakika ni a iya karatuna da binciken da na yi ban ga wata fa’idar hakan ba
Shaikh Rigacikin ya kuma ce hadin kan al’ummar Musulmi wajibi ne
Ya yi kira ga Alkalai da su rika yanke hukuncin Shari’a a kan lokaci ana ajiye mutane a gidan wakafi ba tare da an yanke hukunci ba
Shaikh Yusuf Sambo Rigacikun ya ce Kungiyar Izalatulbidi’a wa’ikamatussunah karkashin Shaikh Sani Yahaya Jingir ta na Nan a kan karantarwar Alkur’ani da hadisin Manzon Allah duk abin da bai sabawa Musulunci ba kungiyar na nan a kai ko yaushe.

About andiya

Check Also

Ododo Bags Champion Newspapers Governor of the Year on Youth, Security Award

By; Imrana Abdullahi Kogi State Governor, Ahmed Usman Ododo, has received another national recognition for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.