Home / Big News / Na Yi Allah Wadai Da Abin Da Ya Faru A Tsakanin Shugabannin Kungiyar ACF 

Na Yi Allah Wadai Da Abin Da Ya Faru A Tsakanin Shugabannin Kungiyar ACF 

….Mun Yi Tir Da Abin Da Ya Faru
Daga Imrana Abdullahi
Wani fitaccen dan Gwagwarmaya Alhaji Umar Husaini, ya bayyana cewa abin da yake faruwa a tsakanin shugabannin kungiyar Tuntuba ta tattawan  Arewa ( ACF) a matsayin abin kunya da yake yin Allah wadai da faruwar hakan saboda lamarin ya batawa dimbin jama’ar arewacin Najeriya rai.
.” Ban ji dadin irin yadda lamarin ya faru ba musamman ma ganin yadda ake kallon su a matsayin jagorori a arewacin Najeriya, amma sai ga shi lamarin ya faru a haka don Allah ta yaya al’ummar arewa da duniya baki daya za su kalle su sakamakon abin da suke aikatawa na rashin kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu shugabanni”, Inji Umar Husaini.
Dan kishin al’umma da ke fafutukar kwato yancin bil’adama Kwamared Umar Husaini ZanZan ya bayyana rashin jin dadinsa game da irin abubuwan da ke faruwa a tsakanin jagororin kungiyar a matakin kasa.
Kwamared  Umar Husaini ZanZan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu a garin Kaduna hedikwatar arewacin Najeriya.
Kwamared ZanZan ya ci gaba da bayanin cewa ta yaya babbar kungiya kamar ta Tuntuba da ake kira, “Arewa consultative Forum”, za a samu jagororin ta sun shiga cikin irin wadannan matsalolin da har ake ta maganganu a kan kudi da sauran takaddama mara dadin ji  ga duk wani dan arewa a ko’ina yake a fadin duniya.
“Idan nan gaba suna son yin wani babban taron su kira manyan mutane daga ki ina a fadin duniya ta yaya za su iya amsa gayyatar da aka yi masu har su halarci taron a nan gaba, bayan ga irin halin da ake ciki a yanzu”.
Don haka muna ba wadannan jagorori na kungiyar Tuntuba ta Arewa shawarar cewa ya dace su hanzarta gyara kan su bayan sun dai daita tsakaninsu ta yadda yan arewa za su yi alfahari da wannan kungiyar a koda yaushe.
Muna fatan don Allah su dubi irin halin da ake ciki a yanzu kada su sake wani abu ya haifar da rushewar al’amuran kungiyar nan ta ADC.

About andiya

Check Also

Norwegian Sovereign Wealth Fund Eyes Partnership with Dangote Group on Africa Investments

  The President/Chief Executive of Dangote Group, Aliko Dangote has held a high-level meeting with …

Leave a Reply

Your email address will not be published.