Home / Big News / Taron Yi Wa Tinubu Addu’a Ya Yi Armashi A Kaduna

Taron Yi Wa Tinubu Addu’a Ya Yi Armashi A Kaduna

…Dole Ne Ayi Wa Shugabanni Addu’a, Inji Tijjani Kaura
Daga Imrana Abdullahi
Sanata Tijjani Yahaya Kaura,tsohon ministan ma’aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriya, ya bayyana cewa a matsayinsa na cikakken dan kasa Nagari ya na da gagarumar dama da ikon zuwa ya hadu da sauran yan Najeriya domin yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara a kowane fanni domin yi wa shugaba addu’a yi wa kasa addu’a ne.
Don haka yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a mutum na yin addu’a ne kai tsaye domin samun ingantaccen tsaro ga kasa da al’ummarta baki daya saboda haka ne na zo nan inda aka taru aka yi wa shugaban kasa addu’a.
Tijjani Yahaya Kaura ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron addu’ar da aka yi a dakin taro na gidan Arewa a cikin garin Kaduna.
Tijjani Kaura ya ce ya kuma zo ne domin ya wakilci Sanata tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Abubakar Yari, a wajen wannan taron addu’a wanda yakasance a kan gaba gaba wajen goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kamar dai yadda na bayyana ne, ” a lokacin da shugaba Tinubu ya zo a shekarar 2023 ya tarar da rufin Najeriya wato yanayin ƙasar baki na cikin wani hali na tabarbarewa wato kusan ko’ina ya bubburme ya huje kuma har ma ya na neman rugujewa baki daya. Lokacin da ya hau mulkin sai yaga cewa lallai lalacewar ta yi yawa kwarai don haka ya na da zabi guda biyu ko dai ya like wuraren da ke da matsalar burmewar domin kada ruwan sama ya rika zubowa domin kada ya lalata cikin Daki ko Dakunan da ba a don ya lalace ko kuma ya cire wannan rufin kwanon ya sake shimfida sabo fil, ta yadda dakin zai gyaru ya kuma dade da kyau da lafiyarsa. Don haka ne dole sai yan Najeriya sun fuskanci yanayin wahalhalun da suke fuskanta, don haka ne nake cewa jama’a tun da har shugaban kasa Tinubu ya dauki wannan matakin ya dace a bisa tsarin adalci a sake ba shi wata damar ta ya cika shekarunsa hudu su zama Takwas kenan domin ya karasa dukkan ayyukansa da ya fara na gyaran Najeriya ta yadda za a samu ingantacciyar nasara mai kasa daya al’umma daya.
Tun da farko da yake gabatar da jawabinsa a dakin taron addu’ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Muktar Ramalan Yero, kira ya yi ga jama’a da su rika gaya wa shugabanni gaskiya a koda yaushe domin ta haka ne za a samu al’amuran kasa su inganta.
Ya kuma yi kiran fadakarwa ga jama’a da su rike gaskiya da amana abin da ya bayyana da cewa babbar hanya ce ta samu ci gaban da kowa ke bukata.
Muktar Yero, ya bayyana taron arewa Think Tank da cewa shi ne karo na Uku da suka yi duk da nufin ci gaban kasa.
An kuma raba wa jama’a Buhunan Shinkafa bayan kammala taron addu’a.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Recalls Redeployed Engineers

    Dangote Petroleum Refinery has approved the recall of engineers previously redeployed across its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.