Home / Big News / An Yi Taron Yi Wa Bola Ahmed Tinubu Addu’ar Samun Nasara A Kaduna

An Yi Taron Yi Wa Bola Ahmed Tinubu Addu’ar Samun Nasara A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
An bayyana daukacin shugabanni masu rike da madafun iko da cewa mutane ne da ke buƙatar ayi masu addu’a ta kwarai domin samun nasarar gudanar da jagoranci su.
Dokta Sule Iko Sani Sami, Marafan Zuru ne ya yi wannan kiran da cikakken bayanin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Hakan ne ya sa aka yi wani gagarumin taron yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a karkashin jagorancin kungiyar arewa Think Tank.
An dai yi taron alarammomin ne da aka yi addu’a bayan karanta Alkur’ani mai girma a dakin taro na Arewa ( arewa house), cikin garin Kaduna.
Dukkan shugabanni na son aiwatar da ayyukan ci gaban rayuwar jama’a da suka hada da harkar Noma, Kiwo,samar da hanyoyi,samar da ingantaccen tsarin samar da lafiya da dai sauran fannoni da damar, don haka ne abubuwan ke dan daukar lokaci suna habbaka da kyautata wa Sanni a hankali.
“Saboda haka ga wanda ya san abin da shugaba Tonubu yake yi a makarantu, Asibitoci da fitar da hanyoyi, musamman wannan ta Sakkwato zuwa Badagiri da aikin titin Jirgin kasa daga Najeriya zuwa kasar jamhuriyar Nijar da sauran hanyoyi da dimbin ayyuka da dama, ana yin su ne domin taimakon arewacin Najeriya don haka lallai ya dace a duba a ci gaba da ba shugaba Tinubu cikakken hadin kai da goyon baya. Don haka abu ne mai kyau Tinubu ya karasa ayyukan da yake aiwatarwa tun da ba wani da za a ce zai yi shekaru hudun kuma, wane ne ma da zai yi aiki fiye da Tinubu abin da ya yi a shekaru hudu.kai tun da dadewa mun fito tsawon shekaru can baya waye ya yi abin da shi wannan yake aikata wa don ci gaban kasa, don haka muke gaya wa jama’a cewa hakki ne kuma adalci ne Allah ya bashi dama ya karasa shekarunsa Takwas domin ba dadewa sai kaga lokaci tuni ya wuce har shekarun Takwas sun kare.
“Don haka a sani fa Bola Tinubu shugaba ne in ka yi masa addu’a ta kirki ta gari zaka gani a cikin kwayar ka  don haka ayi wa shugaba addu’a ta kwarai. Allah ya bashi ikon da zai ci gaba da yin Ayyukan alkairi, haka ma gwamnonin Mu Allah ya ba su dama da dukkan ikon yin maganin matsalolin da ke damuwar mu, Allah ya ba Gwamnatin nan Sa’a ya kawo mana zaman lafiya”.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Recalls Redeployed Engineers

    Dangote Petroleum Refinery has approved the recall of engineers previously redeployed across its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.