Wata Mai Taimakon Jin Kai Ta Cike Ramuka NUJ Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
A Kaduna Arewacin Nijeriya wata mai taimakon rayuwar jama’a Barista A’ishatu Sule, ta yi aikin cike ramun da suka dade suna kawo cikas a duk lokacin da mutane suka zo shigowa cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna.
Hakika jama’ar da suke shigowa wannan babban Ofishin shiyya tare da na Jihar Kaduna suna samun matsala sakamakon irin yadda Ruwa ya Gine hanyar shiga cibiyar ta yan jarida da ake cewa NUJ.
Ita dai wannan Lauya da ta yi wannan taimako na mota uku na Dutsen ciko ta ce ta yi wannan taimako ne domin Tallafawa rayuwar jama’a.
Kamar yadda ta ce, ta shigo harabar wannan cibiyar ne domin gurza wadansu takardu tare da yin fotokwafi sai ta lura da wadannan ramuka a tsakiyar hanyar shigowa wannan babban ofishi, da ke haifarwa masu shiga rashin jin dadi da kuma rashin jin dadin gani wannan me yasa ta ga dacewar yin wannan aikin.
Batista Sule wadda ta kasance Manajan darakta ce a wurin mota jiki da gudanar da tarurruka da kuma dakunan saukar baki ta ci gaba da cewa lokaci ne da yan Nijeriya ya dace su rika gudanar da ayyukan raya kasa domin jin dadin jama’a cikin irin dukiyar da Allah ya ba su domin inganta rayuwar marasa karfi da ke cikin al’umma.
“Lokacin da na shigo wannan cibiyar manema labarai ta Kaduna na ga irin yadda ruwa ya zaizaye hangar shigowa wanda sanadiyyar hakan aka samu ramuka sosai don haka Naga dacewar in cike wannan ramuka domin jama’a su ji dadin wucewa”.
“Ina yin kira ga masu hannu da shuni da ke cikin al’umma da su rika duba irin wadannan abubuwa domin suma su taimaka kamar irin wannan ko kuma ta wadansu hanyoyi na daban ta yadda rayuwar dan adam za ta inganta a kowane fanni na rayuwa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar yan jarida reshen Jihar Kaduna kwamares Adamu Yusuf, yabawa wannan Lauya ya yi bisa hangen neman da ta yi inda ya yi mata addu’ar ci gaba da samun babban rabo daga Allah.
Shima mai wurin buga takardu a cibiyar yan jaridar Injiniya Sani Jimoh mai cibiyar yanar Gizo na Sanjim, Wannan Lauya A’Isha Sule daya ce daga cikin masu yi masa ciniki da ta nuna damuwarta na ceton wannan wuri daga cikin halin da yake ciki da ya shafi dukkan kowa.