Home / Big News / Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Samu Matsala Ne Tun Shekarar 1985 – Lauya Mai Nasara

Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Samu Matsala Ne Tun Shekarar 1985 – Lauya Mai Nasara

Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Samu Matsala Ne Tun Shekarar 1985 – Lauya Mai Nasara

Imrana Abdullahi
Lauya  Dokra Mai Nasara Kogo Umar ya bayyana cewa matsalar tattalin arzikin Nijeriya ya shiga wani mummunan yanayi ne tun a shekarar 1985 wato shekaru 35 da suka gabata kenan.
Ya bayyana cewa kusan dukkan bangarorin tattalin arzikin Nijeriya sun ruguje, inda ya ce kama daga harkar Noma, Masana’antu, harkar fitar da kaya kasashen waje da sauran bangarori da dama duk sun ruguje baki daya”, inji Mai Nasara Kogo Umar.
Ya ci gaba da bayanin cewa matakan kananan hukumomi a Nijeriya sun rushe domin ba su iya yin komai sai jiran daunin kudin da za a ba su daga asusun rabon arziki na wata wata.
Dokta Mai Nasara Kogo Umar ya bayyana hakan ne a cikin shirin Bakin Zaren na gidan Talbijin na kasa NTA mai yada sharrinsa a harshen hausa, inda aka tattauna da shi a kan batun kasafin kudin shekarar 2021 mai zuwa.
” Ai tun da aka mayar da kananan hukumomi karkashin asusun hadin Gwiwa shi ne nan sai lamarin ya zama ba komai a karamar hukuma domin duk sun karye Bali daya, wasu ma basa iya tsinanawa kansu komai sai da kyar suke albashi”.
Ta yaya za a ce wai akwai tsarin ci gaban kasa na shekaru amma a kowace shekara sai an yi kasafin kudi, bayan an san kasafin wani lokacin ma tsammani ne na za a samu kudin bashi ko na Tallafi daga wadansu wurare, to, ina kasafin yake?
“Muna kira ga jama’a da su rika rikon amana a kan dukkan matakin da mutum ya samu kansa a kai a harkar rayuwa domin sai an rike Amana ne sannan za a samu ci gaban kasa”.
Ya kara da cewa shirin Gwamnati na bayar da bashi ga jama’a ba ciyar da kasa gaba ba ne wannan domin lamarin sunansa bashi, a dai samawa jama’a aikin yi a kuma samu jadawalin bayanan yan kasa baki daya a karfafa hukumar samar wa jama’a aikin yi ta NDE.
” A koyawa mutane yadda za su iya kamo Kifi da kansu daga cikin ruwa ba yadda za su ci kifi ba kawai, a dai tabbatar da wani tsari ga yan kasa da zai zamar masu mai amfani”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.