Related Articles
Gwamnatin Borno Ta Amince Da Kashe Kudi Biliyan 6, Ayyuka 18
Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zullum a ranar Laraba ta amince da a kashe kudi naira biliyan shida domin aiwatar da ayyuka Goma sha Takwas (18) da kuma ayyukan kula da harkokin tsaro a cikin Jihar baki daya.
Kwamishinan yada labarai, Baba Kura Abba Jato, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a karshen taron majalisar zartaswar Jihar karo na farko a shekarar 2021 wanda Gwamnan Jihar ya jagoranta a dakin taro na cikin gidan Gwamnati.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa majalisar zartaswar ta amince da kudi miliyan dari 352 domin Tallafawa ayyukan tsaro na hadin Gwiwar Mafarauta, masu aikin sa kai domin tabbatar da tsaro. Sai aikin gyaran titin Maiduguri zuwa Damboa a kan kudi naira miliyan 658 sai kuma aikin ginin Tashar Bama hade da shaguna da kuma aikin karamar kasuwar da ke tattare da shaguna a zagaye da ita.
Sauran ayyukan sun hada da fadada aikin titin cikin gari na Beniskeikh a kan kudi naira miliyan 231, sai aikin titin da ya taso daga Ramat zuwa Wulari mai hade da aikin hanyoyin ruwa duk a kan kudi naira miliyan 237 sai kuma aikin titin Ngomari na tsohuwar Tashar Jirgin sama.
Daga cikin abin da majalisar zartaswar ta amince da shi ya hada da aikin ginin wadansu bangarori biyu na asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Borno a kan kudi naira biliyan 1.6, sai aikin ginin shaguna a Bulunkutu, sai ginin ajujuwa 33 da za a gina bene mai hawa biyu a manyan makarantu a Buratai kan kudi naira miliyan 252.
Sai kuma aikin wurin koyon Walda da ayyukan sarrafa karfe da koyon gyaran mota a makarantar kwalejin Gwamnati da le Gwange da kuma sayen Litattafai ga daukacin makarantun Jihar da kuma aikin ciyar da daliban makarantu a Jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa majalisar zartaswar ta kuma amince da aikin ginin ajujuwa 4 da za a gina bene mai hawa biyu da ya hada da dakunan kwana uku a kowace makaranta da suka hada da Mafa, da za a sa yi fala falan Wutar lantarki Dubu 1,500 domin gyaran na’urar raba hasken lantarki mai karfin 33Kva da layin lantarki na Mafa da Dikwa zuwa Gamboru Ngala, Bama zuwa Gowza a kan kudi naira miliyan 520.
Sai sayen kayan koyawa dalibai da ke karatun koyon sana’o’i a Kwalejin Njimtilo a kan kudi naira miliyan 159.
Sauran sun hada da sayen kayan aikin Koyar da kimiyya a dakunan Gwaje gwaje na kwalejin Njimtilo, a kan kudi naira miliyan 84 sai aikin ginin karamar cibiyar kula da lafiya matakin farko a ta Wulari tare da ginawa ma’aikata gidaje a kan kudi naira miliyan 127.
Sai aikin ginin bene hawa daya guda uku mai dakuna 2 da kuma bene mai hawa daya kuma mai daki daya a kan titin Kano, da kuma ginin babban masallaci a Ngala da sayen Masara da amfanin Gona a karkashin shirin ajiyar abinci na Buffa.