Related Articles
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Ya Bude Aikin Tituna A Ribas
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da bude sababbin titunan da Gwamnan Jihar Ribas Nyeson Wike ya gina .
” Gwamnonin jam’iyyar PDP a halin yanzu suna yin aiyuka domin ci gaban jama’a a Jihohin Jihohin suke yi wa jagoranci, hakika mun san cewa muna yin bakin kokarinmu domin cika alkawuran da muka daukarwa jama’a na samar masu da kyakkyawan shugabanci”.
Ya ci gaba da cewa dole ne mu kara kaimi wajen yin irin wadannan ayyukan ba wai kawai don mu samu amincewar mutanenmu ba, a’ a har ma domin tabbatar da bayyana godiya da Allah da ya ba mu wannan damar jagorantar jama’a a Jihohinmu.
Hanyar da kawai mutum zai bayyana godiyarsa ga Allah ita ce yi wa jama’ar da suka ba shi wannan dama ya yi masu aiki tare da samar da kyakkyawan shugabanci bakin iya karfinka