Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Aikewa Majalisar Dokoki Sunayen Mutane Uku

Gwamna Zulum Ya Aikewa Majalisar Dokoki Sunayen Mutane Uku

Gwamna Zulum Ya Aikewa Majalisar Dokoki Sunayen Mutane Uku
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya zabi mutane uku da za su yi aiki a hukumar kula da ayyukan majalisar dokokin Jihar.
Mutanen uku sun hada da Bukar Malam Bura, Aliyu Mamman Kachallah da kuma Aliwa Bukar da za su yi aiki a matsayin masu aiki tare da hukumar da ke kula da aikin majalisar dokokin Jihar wadanda daman su ba asalin ma’aikatan hukumar ba ne.
Mai ba Gwamnan shawara a kan harkokin samar da kyakkyawar dangantaka da tsare tsare, Malam Isa Gusau, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya sanyawa hannu aka aikawa manema labarai , cewa Gwamna Zulum a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 13 ga watan Janairu, 2020 da aka aikawa shugaban majalisar dokokin Jihar, inda ya bukaci cewa majalisar ta amince da sunayen mutanen da ya aike mata.
“Kamar yadda dokar kasa ta ba ni dama yadda yake kunshe a cikin sashi na 198 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, ina rokon wannan gida mai albarka da ku amince da nadin wadannan mutane, domin su yi aiki a hukumar kula da aikin majalisar dokoki ta Jiha, mutanen sun hada da Honarabul Bukar Malam Bura, Honarabul Aliyu Mamman Kachallah da Honarabul Aliwa Bukar.
Ina son yin amfani da wannan dama in isar da godiyata ga shugabanni bisa goyon baya da kuma aiki tare da a koda yaushe kuke ba mu, daga wannan majalisar. Ina baku tabbacin hadin kai da goyon bayan bangaren majalisar zartaswa”, Zulum ya rubuta a cikin takardar da ya sanyawa hannu.
 Hukumar da ke kula da aikin majalisar dokoki ta Jiha wata hukumace da doka ta amince a samar da mutanen da za su yi aikin tafiyar da mulki, tsare tsare, bincike da suka abubuwan da za su taimaka da suka kasance dole ga zababbun yan majalisa su aiwatar da ayyukansu a matsayin masu wakiltar mazabunsu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.