Home / Labarai / Bayan Shekaru 22, Wani Gurgu Ya Samu Tallafin Keken Guragu Na Zamani

Bayan Shekaru 22, Wani Gurgu Ya Samu Tallafin Keken Guragu Na Zamani

Bayan Shekaru 22, Wani Gurgu Ya Samu Tallafin Keken Guragu Na Zamani
Mustapha Imrana Abdullahi

 

Wani bawan Allah mai tausayi da jin kan jama’a da ke aiki a kamfanin Samar da Maltina ya taimakawa wani bawan Allah mai suna Malam Aminu Gurgu Malumfashi domin ya samu saukin rayuwa, bayan kwashe shekaru 22 ya na gungurawa haka nan a kasa.
Shi dai wannan bawan Allah mai fama da nakasa da ya fito daga garin Malumfashi karamar hukumar Malumfashi cikin Jihar  Katsina, mai suna Aminu Gurgu, ya samu dacewa da samun saukin rayuwa bayan da wani bawan Allah da ya kasance mabiyin addinin Kirista ya Sanya kudinsa wuri na gugar wuri ya sayo keken Guragu irin na zamani mai amfani da hasken rana domin Tallafawa Aminu Malumfashi.
Danladi John ya shaidawa manema labarai cewa a koda yaushe suka hadu da Aminu Gurgu yana yi masa gaisuwa kuma bai taba tambayarsa kudi ba sai dai su gaisa ana dariya da annashuwa tare da Juna.
Kamar yadda Aminu ya ce suna dai gaisawa ne da Danladi John wanda sai daga baya ne ya gane cewa yana aiki ne da wani kamfani mai zaman kansa a Kaduna.
 “Hakika na samu wannan nasara ne lokacin da muka hadu da abokina a gaban wurin sayar da kaya na “Chicken Republic” da ke  Barnawa, ina gaishe shi duk lokacin da yazo wannan wuri sai wata rana ya tambaye ni sunana, sai yake tambaya ta yaya na kasance mai fama da nakasar Gurgunta kuma Bana amfani da kujerar da ke taimakawa mutane iri na masu nakasa, sai na gaya masa cewa babu ce ta kawo hakan. Sai muna dai yin magana a duk lokacin da yazo wannan wurin da yake gani na sai kawai a jiya ya ba ni mamaki kwarai lokacin da ya kawo mini wannan babban  Keken zamani, bayan  na kwashe shekaru 22 ina tafiya ba Keke, sai ga shi na samu na zamani daga wannan Bawan Allah.
A lokacin da aka tuntubi Mista Danladi John da ke aiki da kamfanin Nigerian Breweries Plc Kaduna wanda da farko ya ki amincewa ya yi magana, amma bayan matsin lamba sai ya ce “Mun saba da Aminu ne saboda ba kamar yadda kowane mai fama da nakasar Gurgunta ba da suke rokon kudi ga dukkan kowa, wannan mutum bai ta ba tambaya ta kudi ba kuma a koda yaushe ya ganni ya na gaishe ni kuma ina ganinsa ya na gungurawa yana jan jiki domin bashi da abin hawa, hakan kuma yana taba mini zuciya, sai na yanke shawarar in bashi mamaki da sayo masa sabon Keken irin na zamani mai amfani da na’urar amfani da hasken rana da zai yi abin da zai yi amfani da shi, kuma ina fatan zai yi amfani da shi kamar yadda ya dace.
Aminu, ya kuma yi kira ga daukacin mawadata da ke cikin al’umma da su rika taimakawa mutane musamman masu fama da nakasa.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.