Related Articles
Shekaru Sama Da Ashirin Babu Wani Abu Na Ci Gaba A Kasar Birnin Gwari – Mai Gwari II
Mustapha Imrana Abdullahi
Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari na II ya bayyana cewa shekaru sama da Ashirin da suka gabata babu wani ci gaban da yankin su ya samu saboda kawai wai sai ace ba su da zaman lafiya.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta bbc hausa.
Ssrkin na Birnin Gwari ya ci gaba da bayanin cewa su na matukar son ganin sun samu ci gaba a fannoni da dama amma a koda yaushe sai a rika cewa babu zaman lafiya a yankin don haka babu komai.
Sarkin dai ya bayyana cewa batun matsalar rashin tsaro a kasar Birnin Gwari lamatin ya fara ne tun a shekarar 1994 da ta gabata.
“Lamarin dai ya fara ne tun a shekarar 1994 lokacin da wasu yan tare hanya sai an ba su kudi in kuma babu sai su rika dukan mutane haka kawai, wannan dalili ne ya sa idan mutane za su yi tafiya sai sun Sanya kudi a aljihunsu saboda in sun tare hanyar duk wanda bashi da kudi zai sha duka”‘ inji Mai Martaba.
Ya kara da cewa bayan nan sai suka koma satar Shanu bayan Sahaun sun kare sai aka koma satar jama’a har inda lamarin yake a halin yanzu da ya zama wata matsalar daban.
“Mu mutane ne masu zaman lafiya koda yake wasu wai sun ce saboda Gwal ne da muke da shi, to ba sai su dauki Gwal din ba su daina kashe mu haka kawai ba gaira ba dalili”.
Mai Martaba Sarkin na Birnin Gwari ya kuma yi bayanin irin yadda aka kaiwa motocinsa hari duk da cewa baya cikin motar, ” kadai ga gilashin motar daga gaba irin yadda aka yi rata rata da shi kuma gilashin ta bangaren inda nake zama ma nan ma sai da aka fashe shi da albarusai baki daya”, inji Sarkin.
Da yake bayani kan cewa ko a kwai masu ba barayi bayanan sirri kuwa ya ce hakan za ta iya yuwuwa sai dai a ci gaba da yin addu’ar neman kariya daga Allah.
“Kuma a ci gaba da addu’a ana kyautata aiki domin ba a san ko wasu daga cikin al’umma suna yi wa Allah laifi ba da har irin wadannan abubuwa ke faruwa hakan, amma ina tabbatar wa da duniya cewa mutanen kasar Birnin Gwari masu son zaman lafiya ne a koda yaushe.