Home / Big News / Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bayyana Ceto Mutane 10 Daga Hannun Yan bindiga

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bayyana Ceto Mutane 10 Daga Hannun Yan bindiga

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bayyana Ceto Mutane 10 Daga Hannun Yan bindiga
Mustapha Imrana Abdullahi
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ne ya bayyana cewa jami’an tsaron Soja ne suka ceton mutanen Goma da aka dauka daga cikin iyalai biyu na rukunin gidajen ma’aikatan filin Jirgin sama da ke Kaduna.
Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya bayyana cewa lamarin dai ya faru ne a gidajen kwana na ma’aikatan filin Jirgin sama da ke Ifira, cikin karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa a yau ranar Laraba 17 ga watan Maris, 2021 an samu nasarar kubutar da mutane 10 da aka sace a Ifira da ke karamar hukumar Igabi cikin Jihar Kaduna.
Ga dai sunayen mutanen da aka ceto kamar haka.
Mista Ilori Sunday
Misis  Celestina Sunday
Mis  Beauty Oshaibie Sunday
Mis  Miracle Sunday
Mis Marvelous Sunday
Mis Destiny Sunday
Mista Samuel Sunday
Mis Deborah Sunday dukkansu yan gida daya ne.
Sai kuma Hajiya Badiyatu Abdullahi Gambo
da Bilkisu Gambo da suma aka sace daga gida daya.
Indai za a iya tunawa maharan sun tsallake katangar rukunin gidajen ne a sanyin safiyar Asabar 6 ga watan Maris 2021, suka kuma sace mutane 10 daga gidaje guda biyu da suke kusa da katangar.
Kamar yadda Kwamishina Aruwan ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El- Rufa’i Rufa’I samu rahoton kubutar da wadannan mutane da murna da farin ciki, wanda sakamakon hakan ya ziyarci wurin da aka ajiye mutanen ana duba lafiyarsu inda ya tattauna da su cikin murna da farin ciki, ya kuma yi masu fatan alkairi a daukacin rayuwarsu nan gaba baki daya.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.