Related Articles
Gwamna Zulum Ya Karbi Rahoton Kwamitin Samar Da Hukumar Kula Da Ilimin Tsangaya
Mustapha Imrana Abdullahi
Kwamitin da Gwamnan Jihar Borno ya kafa domin yin aikin samar da kara inganta ilimin tsangaya ya gabatar da rahotonsa ga Gwamnatin Jihar.
Kwamitin dai ya zayyana a cikin rahoton irin yadda ya dace a samar da sabuwar hukumar kula da ilimin tsangaya domin yin gyara ga harkar Almajiranci.
Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Talata ne ya karbi rahoton kwamitin mai shafuka 76 da ya fayyace yadda za a samar da ingantaccen ilimin Tsangaya da zai rika dubawa da kuma tantance lamarin ilimin Tsangaya a cikin Jihar, da ake kira ilimin almajirci.
An dai gabatarwa Gwamna Zulum rahoton ne a ranar Talata a Maiduguri.
A watan Nuwamba ne na shekarar 2020, da ta gabata ne Gwamna Zulum ya kaddamar da kwamitin da aka Dorawa alhakin samar da wani tsarin da za a iya amfani da shi wajen kawo karshen yin barace barace a kan tituna tare kuma da wulakanta kananan yara ta hanyar wai samun ilimin almajirci da ake kira Tsangaya.
Kwamitin dai na da mambobi daga kowane bangare na malaman addinin Islama, karkashin shugabancin Khalifa Aliyu Ahmad Abulfatahi.
Bayan gabatar da tattaunawa da jama’a masu yawa lamarin da ya hada da yin taron jin ra’ayin jama’a da kuma mutanen da Allah ya horewa kwakwalwa da tunani da duk suka gabatar da gudunmawarsu ga kwamitin bayan nan ne aka samar da rahoton.
Da yake gabatar da rahoton Shikh Abulfatahi, cewa ya yi za a Dorawa hukumar kula da dukkan al’amuran ne da aka amince da su a matakin kwamitin da kuma dukkan manufofin Gwamnati baki daya.
Da yake karbar rahoton Gwamna Zulum ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa game da aikin kwamitin sakamakon irin kyakkyawan aikin da suka yi.
Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa za a duba rahoton sosai za kuma a dauki dukkan matakan da suka kamata ta hanyar yin amfani da abubuwan da kwamitin ya zayyana a cikin rahotonsa.
Zulum ya kudiri aniyar yin amfani da tsarin Gwamnatin tarayya na Koyar da ilimin sana’o’i da yin hadin Gwiwa da hukumar da ke kula da ilimin kere Kere ta kasa ( NBTE) domin cimma burin samar da ilimin addini da na Boko baki daya Wanda hakan zai bayar da dama ga wadanda suka halarci makarantun tsangaya su wuce zuwa manyan makarantun ilimi na kasa.