Home / News / Jhar Bayajidda: Za Mu Dogara Da Harkar Noma – Kabir Ado Daura

Jhar Bayajidda: Za Mu Dogara Da Harkar Noma – Kabir Ado Daura

Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon dan majalisar dokokin Jihar Katsina honarabul Kabir Ado Daura ya bayyana cewa kokarin da suke yi na a kirkiro da Jihar Bayajjida daga cikin Jihar Katsina da wani bangare na Jigawa duk domin ci gaban al’ummar kasa ne baki daya.
Honarabul Kabir Ado Daura, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan mikawa Kwamitin majalisar Dattawa da ke aikin gyaran kundin mulkin kasa da ya zauna a Kaduna.
Kabir Ado Daura ya ci gaba da bayanin cewa sun gabatar da bukatar neman Jihar Bayajidda ne a gaban wannan kwamitin bisa dogaro da abin da kundin tsarin mulkin kasa ya ce na damar a nema, sannan kuma akwai ingantaccen tattalin arzikin kasa da harkar Noma da za a dogara da shi Waken rike Jihar idan Gwamnati ta kirkiro ta.
“Hakika muna da arzikin Noma a wannan yankin da ya hada da aikin Noma wanda shi kadai kawai ya isa Jihar Bayajidda ta dogara da kanta idan an yi kirkiro ta, kuma akwai arzikin kiwo a yankin Daura da kuma yankin da za mu hade da su daga Jihar Jigawa domin tabbatar da inganta rayuwar al’ummar Jihar Bayajidda da kasa baki daya”. Inji shi.
A lokacin da yake ganawa da manema labaran akwai mutanen da suka wakilci yankin da suke neman hadewa daga Jihar Jigawa, sauran kananan hukumomin da suke cikin yunkurin samar da Jihar Bayajidda sun hada da Daura,Mai’Aduwa,Baure,Sandamu da Zango sauran su ne Mashi, Mani, Dutsi da sauran yankuna a yankin Daura wanda muna da tabbacin cewa za mu iya dogaro da kan mu da harkar Noma, wanda duk duniya sun san da hakan akwai Noma a kasar Daura baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.